Labari da dumi: Mun mayar wa da CBN N19.3bn ta albashin Kogi da Bello ya boye, EFCC

Labari da dumi: Mun mayar wa da CBN N19.3bn ta albashin Kogi da Bello ya boye, EFCC

  • Hukumar EFCC ta sanar da cewa ta mayar wa babban bankin Najeriya kudi har N19.3 biliyan kudin jihar Kogi da ta kama a wani asusun banki
  • Kamar yadda wasika daga babban bankin Najeriya ta nuna, ta samu kudin wanda wancan bankin ya tura mata za a mayar da su Kogi
  • A kwanakin baya ne EFCC ta kama wasu kudi har N19.3b na kudin albashin jihar Kogi wanda gwamnatin Yahaya Bello ta kwashe tare da zuba su a wani asusu

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta mayar da N19.3 biliyan kudin jihar Kogi wanda gwamnatin jihar ta boye zuwa babban bankin Najeriya.

Hukumar tun farko ta sanar da yadda mulkin Gwamna Yahaya Bello ya kwashe kudin tare da dankara su a wani asusun banki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

Labari da dumi: Mun mayar wa da jihar Kogi N19.3bn da aka boye, EFCC
Labari da dumi: Mun mayar wa da jihar Kogi N19.3bn da aka boye, EFCC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily trust ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kogi ta musanta boye kudin inda ta zargi EFCC da zabga karya.

Amma a takardar da Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ya fitar, ya ce kudin an mayar da su zuwa babban bankin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babban bankin Najeriya ya amsa samun kudi har N19.3 biliyan wanda EFCC ta samo daga gwamnatin jihar Kogi bayan ta boye su a asusun wani banki. Wannan sai ya dakatar da gangami tare da musun da gwamnatin jihar ke yi na cewa babu wani kudi da aka samo daga wurin ta."
"A wata wasika mai kwanan wata 9 ga Nuwamban 2021, babban bankin Najeriya ya sanar da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, cewa sun samu kudin," yace.

Wani bangare na wasikar ya ce:

"Mayar da kudin ya zama biyayya ga hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas na ranar 15 ga Oktoban 2021 inda kotun ta umarci a saki asusun bankin yadda za a iya mika kudin zuwa CBN. Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ne ya bayar da umarni.

Kara karanta wannan

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

"Hukumar ta sanar da kotun cewa,hukumar bankin da kudin ya ke ta tabbatar da wanzuwarsu."

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta garkame wasu kadarorin da tsohon darektan asusai na sojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Tahir Yusuf (Rtd) ya mallaka.

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ke da kadarori a Zaria da Kaduna wadanda aka garkamesu tun kwanakin karshen mako wasu kuma ranar Laraba bisa zarginsa da almundahanar N2bn.

Majiyoyi sun nuna yadda ya ke da kadarori kamar su Otal din Emerald da ke Zaria, wasu gine-gine 2 da ba a kammala ba a Zaria da Kaduna da kuma gidan buredin Bitmas da ke Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel