Da Ɗuminsa: Ma'aikatan sufurin jiragen ƙasa sun janye yajin aiki

Da Ɗuminsa: Ma'aikatan sufurin jiragen ƙasa sun janye yajin aiki

  • Hukumar sufurin jiragen kasa ta dakatar da yajin aikin jan kunne na kwanaki uku da ta fara a ranar Alhamis da ta gabata
  • Hakan ya biyo bayan cimma matsaya da aka yi tsakanin shugabannin ma'aikatan da ma'aikatar sufuri ta tarayya a Abuja
  • Ma'aikatar sufurin ta dauka alkawarin duba tsarin albashin ma'aikatan tare da wasu lamurran walwala da jin dadinsu kamar yadda suka bukata

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa (NRC), ta dakatar da yajin aikin da ma'aikatan ta suka fada na tsawon kwanaki uku, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan taron da suka yi a ranar Juma'a da hukumar NRC da kuma wani da hukuma tayi da ma'aikatar sufuri ta tarayya a Abuja.

Read also

Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki

Da Ɗuminsa: Ma'aikatan sufurin jiragen ƙasa sun janye yajin aiki
Da Ɗuminsa: Ma'aikatan sufurin jiragen ƙasa sun janye yajin aiki. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

A wata takarda da aka fitar bayan taron, ta bayyana cewa kwamitin zai sake duba tsarin aikin ma'aikatan.

Shugaban manyan ma'aikatan NRC, kwamared Aliyu Manasara da shugaban ma'aikatan jiragen kasan, kwamared Innocent Ajiji a madadin kungiyoyin ne suka yi magana.

A yayin taron gwamnati taa kara da amincewa kan cewa a karba bayanan tsoffin ma'aikatan da suka rasu kuma a biya su hakkinsu.

An kara da aminta da cewa, dukkan direbobin jiragen kasan za a basu inshora kamar fasinjoji da kayayyakin da ke ciki. Za a kara musu albashi kuma za a gaggauta tabbatar da karin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, yajin aikin da aka sanar da fara shi a daren Laraba, ya gurgunta al'amuran sufuri a fadin kasar nan.

Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki

Read also

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

A wani labari na daban, karakainar jiragen kasa a fadin kasar nan ta tsaya na tsawon kwanaki uku sakamakon yajin aikin jan kunne da ma'aikatan hukumar sufurin jiragen kasa suka fara a fadin kasar nan.

Yajin aikin jan kunnen wanda hukumar kula da sufurin jiragen kasa, NRC ta fara zai kwashe tsawon kwanaki uku ne, daga 18 zuwa 20 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta wallafa cewa, kungiyar ma'aikatan ta bayyana fadawarta yajin aikin ne bayan sun bukaci karin albashi da wasu bukatu nasu.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya gayyaci kungiyoyin kwadago zuwa wani taro a ranar Asabar wanda suka tashi dutse a hannun riga.

Source: Legit.ng

Online view pixel