Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki

Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki

  • Hukumar sufurin jiragen kasa, NRC, ta fada yajin aikin jan kunne na tsawon kwanaki uku daga daren Laraba
  • Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, duk da yajin aikin, kada ma'aikatan su bari a barnata musu kayayyakin hukumar
  • Sun fara yajin aikin ne bayan sun mika bukatar karin albashi amma an ki cikawa, sun yi taro da Amaechi kuma aka tashi dutse hannun riga

Karakainar jiragen kasa a fadin kasar nan ta tsaya na tsawon kwanaki uku sakamakon yajin aikin jan kunne da ma'aikatan hukumar sufurin jiragen kasa suka fara a fadin kasar nan.

Yajin aikin jan kunnen wanda hukumar kula da sufurin jiragen kasa, NRC ta fara zai kwashe tsawon kwanaki uku ne, daga 18 zuwa 20 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

ICPC: An bankado sama da ma'aikata 50 masu amfani da satifiket da shekarun bogi

Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki
Karakainar jiragen kasa ta tsaya a Najeriya, ma'aikatan hukumar sun tafi yajin aiki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta wallafa cewa, kungiyar ma'aikatan ta bayyana fadawarta yajin aikin ne bayan sun bukaci karin albashi da wasu bukatu nasu.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya gayyaci kungiyoyin kwadago zuwa wani taro a ranar Asabar wanda suka tashi dutse a hannun riga.

An sake yin wani taron da hukumar NRC amma hakan bai sauya hukuncinsu na tafiya yajin aikin ba.

Tun ranar Talata hukumar NRC ta sanar da dukkan manajojin ta da mashiryanta kan cewa su fada yajin aiki ta hanyar daina daukar fasinjoji tun daga tsakar daren Laraba.

A wata takarda da manajan daraktan NRC, Injiya Fidet Okhiria ya fitar a ranar Talata, ya yi kira ga dukkan manajojin yankuna da kuma jami'an hukumar kan cewa akwai bukatar a baiwa kadarorin sufurin jiragen kasan kariya har a yayin da ake yajin aikin.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Takardar ta bukaci dukkan jami'an da ke yawo da jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna, Warri zuwa Itake da Legas zuwa Ibadan da su mayar da jiragen wuri mai kyau inda ba za a barnata su ba.

Babban sakataren kungiyar ma'aikatan jiragen kasan, Kwamared Sugun Esan, ya ce sun fara yajin aikin da gaske kuma ranar Alhamis za a gane hakan kiri-kiri.

Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu

A wani labari na daban, Manajan daraktan hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria, ya musanta rade-radin da ke ta yawo na cewa 'yan ta'adda sun kai wa jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna farmaki.

Okhiria wanda ya zanta da Daily Trust ta wayar salula, ya tabbatar da cewa wani sashi na layin dogon ne aka lalata.

Sai dai, ya alakanta lamarin da mabarnata masu lalata kayan gwamnati inda ya ce ana bincike domin bankado abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

Asali: Legit.ng

Online view pixel