Yan sanda sun gudu da kafafunsu yayinda yan acaba suka kai musu hari kan kashe abokinsu

Yan sanda sun gudu da kafafunsu yayinda yan acaba suka kai musu hari kan kashe abokinsu

  • Rikici ya sake kaurewa tsakanin jami'an yan sanda da matasa yan achaba a garin Akuren jihar Ondo
  • Yan achaba sun zargi wani jami'in dan sanda da bindige abokin aikinsu har lahira ba gaira ba dalili
  • Akalla mutum uku sun mutu yanzu a unguwar Arakule dake birnin Akure, jihar Ondo

Akure - Wasu masu sana'ar tuka babur a Akure, birnin jihar Ondo sun kai farmaki ofishin yan sanda dake Arakule kan kashe musu abokin aikinsu da wani dan sanda yayi.

Masu baburan wadanda aka fi sani da yan achaba sun dira Division A na yan sanda kuma suka farmaki jami'an.

Da dama cikin yan sanda sun arce da gudu yayinda matasan suka dumfaresu.

TVC ta ruwaito cewa yan achaban sun rusa katangan ofishin yan sanda.

Kara karanta wannan

An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda

Yayinda wasu yan sanda ke kokarin hayewa katanga su gudu, wasu na laluben motocin da zasu gudu da su.

Yan achaban sun bukaci a bayyana musu dan sandan da ya kashe musu aboki.

Yan sanda kashe dan achaba
Yan sanda sun gudu da kafafunsu yayinda yan acaba suka kai musu hari kan kashe abokinsu Hoto: Ondo State
Asali: UGC

Menene ainihin abinda ya faru?

A riwayar TheNation, an tattaro cewa yan achaba sun fara zanga-zanga ne lokacin wani direba ne ya buge mutum biyu; dan babur da dan kasuwan Cocoa a Akure, jihar Ondo.

Rahoton ya nuna cewa dukkansu biyu suka mutu kai tsaye.

Bayan haka sai wani jami'in dan sanda ya harba bindiga sama don tarwatsa masu zanga-zanga, amma sai harsashin da ya harba ya kashe wani dan achaba kuma.

Sai dan sandan ya gudu cikin ofishin yan sandan A Division kuma yan achaban suka kure masa gudu.

Kara karanta wannan

An samu fashewar bama-bamai biyu a Kampala, babban birnin kasar Uganda

Daya daga cikin masu zanga-zangan yace kawai a fito musu da dan sandan da yayi harbin.

Yan sanda suka fara harbi

Yayinda masu zanga-zanga ke kokarin shiga ofishin, yan sanda suka fara harbi, hakan ya sake fusata matasan inda suka fara jifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel