'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie

'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie

  • Mutane sun shiga tashin hankali akan yadda ‘yan bindigan Katsina su ka fara sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar radiyo ta Walkie Talkie
  • Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya ce sakamakon yadda gwamnatin ta datse kafofin sadarwa ne ya sa ‘yan binding an su ka nemo wata mafitar
  • Inuwa ya ce duk da tsananin matakan tsaro da gwamnatin jihar ta sa, ‘yan bindiga su na ta nemo hanyoyi iri-iri don kawo cikas ga zaman lafiyar jihar

Jihar Katsina - ‘Yan bindiga masu harkokin su a jihar sun koma amfani da wayar salula mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie, lamarin da ya firgita jama’a da dama.

Premium Times ta bayyana yadda Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya ce yanzu ‘yan bindiga sun sauya salo.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Duk da datse kafofin sadarwa da gwamnatin ta yi, ‘yan bindiga sun nemo wani zabin wanda su ke ganin zai zama hanyar sadarwa tsakaninsu.

'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie
'Yan bindigan Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

A watan Satumba gwamnatin ta yanke hukunci datse kafofin sadarwa a kananun hukumomi 13 a jihar sakamakon yadda rashin tsaro ya tsananta, PremiumTimes ta ruwaito.

A wata tattaunawa da manema labari su ka yi da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce ‘yan bindiga su na iyakar kokarin ganin sun kawo cikas ga zaman lafiyan jihar.

A cewarsa:

“Duk da tarin nasarorin da aka samu, wajibi ne a kula da yadda ‘yan bindiga suka zama cikas na farko da su ke addabar jihar Katsina.
“Su na kai farmaki ga masu ababen hawa don yashe musu man fetur sannan har bincike kauyaku su ke yi don samun kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

“Yanzu babban abin tashin hankalin da su ka tsiro da shi shine amfani da wayar salula wacce ta ke amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie.”

Inuwa, wanda shugaban kwamitin tsaro ne a jihar ya ce yanzu haka jami’an tsaro su na iyakar kokarin kamo ‘yan bindigan da ke amfani da wayar salular ta Walkie Talkie din.

An kama ‘yan bindiga 724 daga watan Maris zuwa Satumba

A cewarsa, tsakanin watan Maris da Satumba, an kama mutane 480 da ake zargin ‘yan bindiga ne, ana bincike akan 42 sannan an yanke wa 216 hukunci.

Ya kara da cewa an samu sauki akan hare-haren da ‘yan bindigan su ke kai wa tun bayan gwamnatin ta shinfida dokokin tsaro a jihar.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel