Ni mace ce, wannan cin fuska ne kuma zan kai ku kotu: Martanin Mai tsaron gidan Iran

Ni mace ce, wannan cin fuska ne kuma zan kai ku kotu: Martanin Mai tsaron gidan Iran

  • Zohreh Koudaei, 32, ta mayar da martani kan maganganun dake yawo na zarginta da kasancewa namiji
  • Yar kwallon ce mai tsaron gidan yan wasan kwallon mata na kasar Iran kuma sun haye gasar kofin Asiya
  • Zohreh tace maganganun da gwamnatin kasar Jordan tayi cin mutunci ne gareta kuma zata dau mataki

Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa na mata ta kasar Iran ta lashi takobin kai hukumar kwallon kasar Jordan bisa tuhumarta da sukayi na cewa namiji ce.

Zohreh Koudaei, ta buge fenariti biyu a wasar da Iran ta lallasa Jordan 4-2 da aka buga a Uzbekistan ranar 25 ga Satumba.

Sakamakon wannan nasara kasar Iran ta haye gasar kofin Asiya karo na farko a tarihi.

An zargi Zohreh Koudaei da namiji ce bayan buge fenariti biyu

An tuhumci mai tsaron Zohreh Koudaei, da kasancewa namiji bayan nasarar da Iran ta samu kan Jordan a wasar kwallo a Satumba, Sport Bible ta ruwaito.

Read also

Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu

A cewar hukumar kwallon nahiyar Asiya AFC, Zohreh Koudaei ta buge fenariti biyu a wasan kuma hakan ya jefa shakku cikin abokan hamayyar Iran.

Hukumar ta kaddamar da bincike kan Zohreh Koudaei domin tabbatar da mace ce ko kuma namiji.

Mai tsaron gidan Iran ta mayar da martani
Ni mace ce, wannan rainin hankali kuma zan kai ku kotu: Mai tsaron gidan Iran ta mayar da martani
Source: Getty Images

Me Zohreh Koudaei tace?

Zohreh a yau ta mayar da martanin cewa ita mace ce kuma ba zata lamunci wannan cin fuska daga kasar Jordan ba.

A cewar jaridar Hurriyet, tace:

"Ni mace ce. Wannan cin fuska Jordan ke yi. Zan shigar da hukumar Jordan kotu."

Martanin gwamnatin Iran

Hukumar kwallon Iran ta saki jawabin ta bakin mai zaben yan kwallo, Maryam Irandoost inda ta bayyanawa Varzesh3 cewa:

"Likitocinmu sun duba dukkan yan wasan sosai gudun irin wannan abu, saboda haka jama'a su kwantar da hankulansu."

Read also

Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai

"zamu gabatar da dukkan bayanan da hukumar kwallon Asiya ke bukata ba tare da bata lokaci ba"
"Wadannan tuhume-tuhumen da ake yi kawai don sun sha kashi hannun yan wasan Iran ne."
"Yan kwallon Jordan na ganin su ya kamata su samu nasara...kuma da suka sha kashi.. sai suka fara kame-kame."

Source: Legit.ng

Online view pixel