Harin ISWAP: Lamari ya yi zafi, sojoji sun sanya dokar hana fita a yankin Borno

Harin ISWAP: Lamari ya yi zafi, sojoji sun sanya dokar hana fita a yankin Borno

  • Rahotanni sun bayyana cewa, an sanya dokar hana fita a yankin Askira Uba na jihar Borno saboda rikicin ISWAP a kwanakin nan
  • Mayakan ISWAP sun addabi mazauna da kuma sojoji a sansanoninsu dake yankin Askira Uba tun farkon makon nan
  • Rundunonin soji sun fatattaki 'yan ta'addan a hare-haren daukar fansa da suka kai kan 'yan ta'addan duk dai cikin kankanin lokaci

Borno - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta kafa dokar hana fita a garin Askira Uba da kewaye a jihar Borno yayin da sojojin ke aikin dakile harin da aka kai a yankin.

A cewar PRNigeria, an tattaro cewa mayakan na ISWAP sun kaddamar da farmaki a Dille wanda cikin gaggawa sojoji suka dakile shi sakamakon hadin gwiwar dakarun sojin sama da na kasa.

Read also

Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

Harin ISWAP: Lamari ya yi zafi, sojoji sun sanya dokar Hana fita a yankin Borno
'Yan ta'addan ISWAP | Hoto: saharareporters.com
Source: Twitter

Dille kauye ne a garin Lassa da ke karkashin karamar hukumar Askira Uba.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa majiya cewa sojojin Najeriya sun ci gaba da taka-tsan-tsan da kuma shirye-shiryen yaki bayan sun samu bayanai kan motsin 'yan ta'adda a wasu kauyuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

“Mun samu bayanan sirrin cewa mayakan na ISWAP sun nufi wata gada ta gabas da kauyukan Wamdeo da Roumirgou a lardin Askira Uba.

“Mun dakile yunkurinsu a yau a wani kauye mai nisa da ake kira Dille da ke karkashin Lassa, ba ma daga kafa saboda muna shirin tunkarar su."

SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar

A wani labarin, 'yan ta'addan Boko Haram sun kwace yankuna biyar na kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Niger kamar yadda Alhaji Ahmed Matane, sakataren gwamnatin jihar ya sanar.

Read also

Da Duminsa: ISWAP ta ƙaryata Rundunar Sojojin Nigeria, ta bayyana adadin sojojin da ta kashe a harin Askira

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Litinin.

Ya yi bayanin cewa, 'yan ta'addan Boko Haram su na rike da yankunan Hanawanka da Madaka a karamar hukumar Rafi, Daily Trust ta ruwaito.

Source: Legit.ng

Online view pixel