SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar

SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar

  • Sakataren gwamnatin jihar Niger, Alhaji Ahmed Matane, ya sanar da cewa yankuna 5 'yan Boko Haram suke rike da su a jihar
  • Kamar yadda yace, akwai yankunan Hanawanka da Madaka a karamar hukumar Rafi, yankunan Kurebe, Gussau da Farina Kuka a Shiroro
  • Ya sanar da yadda 'yan Boko Haram ke yawo gaba-gadi a yankunan dauke da miyagun makamai kuma suna saka dokoki
  • SSGn ya ce jihar Neja ta kashe sama da N2 biliyan wurin yaki da ta'addanci a cikin shekaru 2 da suka gabata, amma har yanzu akwai kalubale

Niger - 'Yan ta'addan Boko Haram sun kwace yankuna biyar na kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Niger kamar yadda Alhaji Ahmed Matane, sakataren gwamnatin jihar ya sanar.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Litinin.

Read also

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna

Ya yi bayanin cewa, 'yan ta'addan Boko Haram su na rike da yankunan Hanawanka da Madaka a karamar hukumar Rafi, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai yankunan Kurebe, Gussau, Farina Kuka a karamar hukumar Shiroro ta jihar, lamarin da ya tirsasa mazauna yankin yin gudun hijira.

SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar
SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Ya ce a halin yanzu 'yan ta'addan na kaiwa da kawowa hankali kwance a yankunan da lamarin ya shafa, dauke da makamai masu hatsari.

Daily Trust ta wallafa cewa, Matane ya ce tuni gwamnatin jihar ta sanar da jami'an tsaro domin su dauka matakan da suka dace a yankin.

"Mun kashe sama da biliyan biyu a kan hukumomin tsaro duk a kan yaki da 'yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun al'amuran da ke faruwa a shekaru 2 da suka gabata."

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

"Za mu cigaba da ba da muhimmanci ga jin dadin jami'an tsaron da aka turo domin basu damar shafe duk wasu masu hannu a miyagun al'amuran da ke barazana ga zaman lafiya, cigaba da daidaituwar siyasarmu.
“Har ila yau, muna kira ga jama'a da su taimaka da bayanai masu amfani kan kaiwa da kawowar miyagu wurin jami'an tsaro saboda a dauka matakin da ya dace.
“Mun kara da tuntubar jami'an tsaro da shugabannin addini tare da masu ruwa da tsaki domin su kira mazauna jihar kan su taimaki gwamnati wurin yaki da ta'addanci," yace.

Matane ya kara da jinjinawa gwamnatin jihar Niger kan kokarin ta na dakile wannan mummunar baraka.

Ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai ta ga karshen kalubalen tsaron da ya addabi jihar.

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

A wani labari na daban, wani malamin makaranta da ke zama a karamar hukumar Damboa a jihar Borno ya bayyana yadda suka yi arangama da mayakan Islamic State in West Africa Province (ISWAP).

Read also

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

Malamin wanda ya bukaci a boye sunan sa, ya ce sun yi gaba da gaba da 'yan kungiyar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Biu ta jihar a cikin kwanakin nan.

Source: Legit.ng

Online view pixel