Ana wata ga wata: Gwamnatin Buhari za ta yi aikin canza taswirar Najeriya

Ana wata ga wata: Gwamnatin Buhari za ta yi aikin canza taswirar Najeriya

  • Gwamnatin Buhari za ta yi aikin samar da sabuwar taswirar kasar saboda a samu hanyoyin dakile wasu matsalolin kasar
  • Shirin sake duba taswirar Najeriya zai taimakawa wajen samar da bayanai da suka dace a wuraren da suka dace
  • Wani jami'in gwamnati ya bayyana yadda gwamnati ta tsara gudanar da aikin, da kuma yadda zai taimaki kasar

Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen sake duba taswirar Najeriya a halin yanzu, wanda gwamnatin Kanada ta samar a shekarar 1970, The Guardian ta ruwaito.

Baya ga haka, aikin duban zai baiwa kasar damar samun sabuwar taswira don samun nasarar tinkarar kalubale daban-daban da ke adawa da himma da kokarin gwamnati na samar da ingantaccen tsarin tsaro.

Ana wata ga wata: Gwamnatin Buhari za ta yi aikin canza taswirar Najeriya
Taswirar Najeriya | Hoto: nigerianfinder.com

Mukaddashin Safiyo Janar na Tarayya (SGoF), Abduganiyu Adebomehin, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kare kasafin kudin shekarar 2020 a gaban kwamitin ayyuka da gidaje na majalisar a harabar majalisar dokokin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

Adebomehin ya bayyana taswirar Najeriya ta yanzu cewa an samar da ita ne ga kasar shekaru 41 da suka gabata, kuma ana bukatar a sabunta ta don tallafawa muhalli, kayayyakin more rayuwa da tsarin zamantakewa da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, kasar za ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen yanke shawarwari masu inganci, da tsara shiri mai kyau da samun nasarar aiwatar da ayyukan da suka dace ga jama'arta ba idan ba a samar da sabon tsarin da zai iya samar da bayanan da suka dace da lokaci ba.

Legit.ng ta tattaro cewa, a kan batun rashin isassun kudi, Adebomehin ya yi nadama da cewa, hakan ya kawo cikas ga samar aikin a yanzu tare da habaka cibiyar tattara bayanai masu amfani.

Ya kuma yi bayanin cewa za a bukaci jirgi mara matuki wanda zai iya tashi na wani dan lokaci don samar da bayanai wajen cika takardan taswirar.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro a Najeriya ta zo karshe da zaran yan majalisu sun amince da kudirin mafarauta, Yahaya Bello

Ya kuma tabbatar da cewa, idan aka samar da kudaden aikin yadda ya kamata, aikin zai iya kawo karin da ya dace wajen bunkasa kudaden shiga na cikin gida na kasar (IGR).

A bangarensa, Shugaban Kwamitin Ayyuka da Gidaje na Majalisar Abubakar Abubakar, ya amince da dacewar bukatar kuma ya nemi a samar wa kwamitin muhimman takardu don karin bayani saboda a samu ingantacciyar hanya.

Yadda Najeriya ta shigo da kifin sama da N100bn daga kasashe 10 na waje cikin wata 6

A wani labarin, duk da yawan ruwa da ake dashi, Najeriya a cikin watanni shida na farkon shekarar 2021 ta kashe Naira biliyan 123.8 wajen shigo da kifi daga waje, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana.

Bayanan na kunshe ne a cikin rahoton kididdigar Kasuwancin Kayayyakin Waje na NBS da ta buga a shafin yanar gizon ta.

Rahoton ya ce an shigo da kifi da ya kai Naira biliyan 48.28 a zangon farko sannan kuma an shigo da na Naira biliyan 75.44 a zango na biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel