ICPC: An bankado sama da ma'aikata 50 da satifiket da shekarun bogi

ICPC: An bankado sama da ma'aikata 50 da satifiket da shekarun bogi

  • Bincike ya bayyana yadda aka kama ma'aikatan hukumar ICPC da satifiket na bogi tare da shekarun bogi suna amfani da su
  • Wannan al'amarin ya ritsa da sama da ma'aikata 50 na hukumar, lamarin da yasa shugaban hukumar ke kokarin daukar mataki maras tsauri
  • Matsalolin sun kama daga banbancin shekaru, takardun hidimar kasa, takardun shaidar kammala karatu da sauransu

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC ta kama ma'aikatan ta da satifiket na bogi da shekarun bogi wanda hakan ya shafa ma'aikata masu tarin yawa, Daily Trust ta tattaro hakan.

Wannan lamarin ya shafi manyan jami'an hukumar masu yawa kuma an gano cewa hakan yasa hukumar ke kokarin daukan sassaukan mataki kan wadanda lamarin ya shafa.

An kama mai kamawa: An bankado satifiket da shekarun bogi na ma'aikatan ICPC
An kama mai kamawa: An bankado satifiket da shekarun bogi na ma'aikatan ICPC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A kalla ma'aikata hamsin na hukumar suka bayyana gaban kwamitin tantance satifiket kuma aka gano cewa akwai banbance-banbbance a takardun makarantarsu da kuma shekarun su.

Kara karanta wannan

Jinsi ba shamaki bane: Injiniya mace 1 cikin maza ta sanar da gwargwamayar da ta sha duk da maraicinta

Me yasa ICPC ta fara tantance takardun ma'aikatan ta?

Daily Trust ta tattaro cewa, tantance takardun ya fara ne bayan an kama wani jami'in hukumar NSCDC mai suna Idowu Olamide da laifin amfani da takardar bogi wurin samun karin girma.

Wani dan cikin gida a hukumar ya sanar da Daily Trust cewa an bukaci hukumar ta fara bincikar ma'aikatan ta bayan wata tsohuwar ma'aikaciyarsu ta koma NDIC amma daga bisani aka kore ta bayan an gano ta na amfani da takardun bogi.

Daily Trust ta tattaro cewa, wannan bukatar ce ta sa hukumar ta kafa kwamitin mutum 3 na bincikar takardun ma'aikatansu.

Kwamitin ya fara da aike wasika ga manyan hukumar su 9 inda ta gayyacesu da su zo domin tantancewa. Sai dai kuwa abun mamakin ya fara ne bayan daraktoci 2 kacal suka tsallake al'amarin.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Ma'ikata sun garkame babban ma'aikatar FG, sun bukaci Buhari ya tsige matar ministansa

Daga nan ne hukumar ta sake gayyatar wasu ma'aikatan ta arba'in da biyu domin tantancewa, a nan ne aka samu sama da ma'aikata hamsin masu matsalar.

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

A wani labari na daban, watakila hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashin gaskiya a Najeriya ta gurfanar da tsohon shugaban cibiyar FIIRO, Chima Igwe a gaban kotu.

A ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, 2021, jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa akwai yiwuwar ayi shari’a da Chima Igwe a dalilin amfani da takardar bogi.

Chima Igwe ya yi amfani da takardun digirin PhD na karya, ya yaudari hukuma, ya yi shekara dai-daya har 18 yana ta karbar albashi ba tare da an gane ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel