Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka

Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka

  • Sanata Ali Ndume na jihar Borno ya koka da yadda miyagun 'yan ta'addan ISWAP ke sake shirya kansu a yankin tafkin Chadi
  • Ndume ya mika ta'aziyyarsa ga rundunar sojin Najeriya tare da jinjina wa Brigediya Janar Zirkusu kan sadaukarwar da ya yi
  • Ndume ya bukaci mazauna yankin Chibok da su kwantar da hankalinsu kuma kada su yi gudun hijra domin karshen ta'addanci ya zo

Shugaban kwamitin kula da sojoji na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya koka kan yadda miyagun 'yan ta'addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) ke sake shirya kansu a yankin tafkin Chadi.

Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa, ya yi wannan koken yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi yayin martani ga harin da 'yan ta'addan suka kai Askira Uba a jihar Borno a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan jita-jitar shirin yiwa Buhari juyin mulki

Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka
Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, soja mai mukamin birgediya janar da wasu sojoji uku ne suka sheka lahira a yayin da aka kashe 'yan ta'adda masu yawa a kan hanyar.

Birgediya Janar Dzarma Zirkusu, wanda shi ne kwamandan runduna ta 28 da ke Chibok suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Askira da ke kudancin Borno domin kai wa sojoji dauki, wadanda ke musayar wuta da 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Ndume ya jajanta wa rundunar sojin Najeriya kan mummunan al'amarin inda ya jinjinawa Birgediya Janar Zirkusu a matsayin na zakakurin soja wanda ya tunkari 'yan ta'adda.

Ya ce duk da dakarun sojin sun ga bayan manyan kwamandojin 'yan ta'addan a Borno, yanayin farmakin Askira abun tashin hankali ne kuma ya yi kira ga jami'an tsaro da su bai wa rundunar sojin duk daukin da suke bukata.

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Dan majalisar ya yi kira ga mazauna yankin Chibok da su kwantar da hankalinsu kuma kada su tashi daga nan. Ya tabbatar musu da cewa rundunar sojin ta na da duk abinda ta ke bukata na yakar ta'addanci.

TheCable ta ruwaito cewa, ya ce, "Ina son bayyana ta'aziyya ta ga rundunar soji kan mutuwar janar a kan titin Chibok.
"'Yan ta'addan ISWAP sun kai farmaki a garin, sun san cewa janar din ne babban kalubalensu a nan. Sun yi kwanton bauna kuma sun saka bam a abun hawansa.
"Zakakurin soja ne wanda ya je yakar 'yan ta'addan. Mutuwarsa ta saka tsoro a zukatan jama'ar yankin. Na san wasu daga cikin mazauna yankin Chibok sun fara tunanin sauya wurin zama.
“Wasu suna son tafiya Mubi da sauran wurare. Muna kira garesu da su zauna. Ta'addancin ya na zuwa karshe.
“Akwai bukatar amfani da sauran hukumomin tsaro wurin bai wa sojoji taimakon da suke bukata. Muna bukatar taimakon kungiyoyi 'yan sa kai.

Kara karanta wannan

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

"Sun bayyana a sama da motoci goma na yaki. Suna sake shirya kansu ne a wurin arewacin Borno, kusa da tafkin Chadi.
"Rundunar sojin ta san da haka kuma sojin sama suna samar da taimako. Daukan fansa ne. Sojojin sun halaka manyan kwamandojin ISWAP kuma suna daukan fansa ne."

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

A wani labari na daban, Samamen da rundunar sojin Najeriya ta kai wa mayakan ISWAP har sansanin 'yan ta'addan ya janyo kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji uku, majiyoyi masu karfi suka sanar da Daily Trust.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace sojojin sun halaka 'yan ta'addan ISWAP yayin arangamar.

Ya ce baya ga kashe 'yan ta'addan, dakarun sojin sun tarwatsa motocin yakinsu. Amma kuma, mayakan ta'addancin a ranar Asabar wurin karfe 9 na safe sun kai farmakin kwanton bauna kan tawagar Birgediya Janar Zirkusu yayin da suke hanyar zuwa garin Askira Uba domin samar da taimako ga dakarun da ake kai wa hari.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel