Afrika ta kudu da sauran birane 6 da Shugaba Buhari ya ziyarta a cikin kasa watanni 2

Afrika ta kudu da sauran birane 6 da Shugaba Buhari ya ziyarta a cikin kasa watanni 2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci akalla manyan birane bakwai na kasashe shida a cikin makonni takwas da suka gabata, kamar yadda rahotanni da dama suka tabbatar.

A halin yanzu, shugaban ba ya Najeriya, yana wata kasa domin halartar wasu taruka da a cewar gwamnati za su amfani kasar baki daya.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku yawan tafiye-tafiye da shugaba Buhari ya yi a kasa da watanni biyu.

Afrika ta kudu da sauran kasashe 6 da Shugaba Buhari ya ziyarta a cikin kasa watanni 2
Tafiye-tafiyen Buhari | Hoto: Buhari Sallau

1. New York, Amurka

A ranar 19 ga Satumba, 2021, Buhari ya bar Abuja zuwa birnin New York na kasar Amurka, domin halartar taro na 76 na Majalisar Dinkin Duniya, ya dawo ranar 26 ga watan Satumba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

2. Addis Ababa, Habasha

A ranar 3 ga Oktoba, 2021, Buhari ya cilla zuwa Addis Ababa don halartar bikin rantsar da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed, a karo na biyu na wa'adin mulki na shekaru biyar, wanda aka gudanar washegarin ranar. Ya dawo ranar 5 ga watan Oktoba.

3.Riyadh, Saudiyya

A ranar 25 ga Oktoba, 2021, shugaban ya dira a Riyadh ta Saudi Arabia, don halartar taron zuba hannun jari wanda Future Investment Initiative Institute ta shirya.

4. Makkah, Saudiyya

Buhari da tawagarsa a ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba sun gudanar da aikin Umrah a Makka kafin su dawo Abuja a ranar 29 ga watan Oktoba.

5. Glasgow, Scotland

Kwanaki biyu bayan dawowarsa daga Saudiyya, shugaban ya kara cillawa zuwa birnin Glasgow na kasar Scotland, domin halartar taron COP26; Ziyararsa ta shida kenan zuwa kasashen waje a shekarar 2021.

6. Paris, Faransa

A ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, 2021, Buhari ya tafi birnin Paris domin ziyarar aiki ta kwana daya a matsayin bakon shugaba Emmanuel Macron a Palais de l’Elysée.

Read also

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

Daga bisani kuma ya halarci taron zaman lafiya na Paris na kwanaki uku tsakanin 11 da 13 ga Nuwamba.

7. Durba, Afrika ta Kudu

Daga birnin Paris, Buhari ya zarce Durban ne a ranar 13 ga watan Nuwamba domin halartar taron IATF karo na biyu da bankin shigo da kaya na Afirka tare da hadin gwiwar hukumar Tarayyar Afirka da sakatariyar yankin ciniki maras shinge ta nahiyar Afirka suka shirya.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya a ranar Talata 16 ga watan Nuwamba.

Kasafin kudin 2022: Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, zasu kashe N3.2 billion wajen tafiye-tafiye kadai a shekarar 2022 da muke dunfara.

Wannan na kunshe cikin kasafin kudin 2022 da Buhari ya gabatar gaban yan majalisa ranar 8 ga Okotba 2021 domin su duba kuma su amince da shi.

A bayanan kudaden, shugaban kasan zai kashe N2.3billion wajen tafiye-tafiye da sufuri na ofishinsa yayinda shi kuma mataimakinsa aka shirya masa N778.2 million.

Read also

Zaben Anambara: Takaitaccen tarihin zaben gwamna tun shekarar 1999 zuwa bana

Source: Legit.ng

Online view pixel