Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

A ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, Hukumar Yaki da Masu Yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, ta yi nasara kan karar da ta shigar kan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar yi wa tsarin fansho garambawul, PRTT, kan wawushe kudin fansho fiye da N2.1bn.

An samu Maina da laifuka kan zargi na 2, 3, 6, 7, 9 da 10 da EFCC suka tuhume shi da aikatawa, kana kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 8 a gidan gyaran hali.

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dudai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC
Kotun Tarayya ta yanke wa Maina hukuncin daurin shekaru 8. Hoto: EFCC
Asali: UGC

Mai shari'a Okon Abang na Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja ya bada umurnin a kwace wasu kudade da kadarori mallakar Maina.

Ga dai jerin kadarori da aka alakanta da tsohon shugaban na PRTT bisa binciken EFCC da umurnin da kotu ta bayar kamar yadda hukumar yaki da rashawar ta fitar.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa Maina hukuncin shekaru 8 a gidan yari bayan kama shi da laifin satar N2b

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Tsabar kudade na Naira Miliyan 300, Naira Miliyan 500 da Naira Biliyan 1.5 da aka saka a asusun ajiyar banki guda biyu

2. Wani gida a birnin tarayya Abuja (Da aka siya da tsabar kudi Dala Miliyan 1.4)

3. Gidaje a Dubai, Hadadiyar Daular Larabawa (wata babban villa a yankin masu hannu da shuni a Dubai) da Amurka.

4. Wani gida na Dallar Amurka Miliyan 2 a unguwar Jabi da ke Abuja

5. Fiye da motocci 50 da ake amfani da su a aikin zirga-zirga a Dubai

6. Wani kamfani mallakar Maina mai suna Colster Logistics, wanda makuden daloli ke shiga

7. Fiye da Naira Miliyan 500 a asusun ajiyar Kangolo Dynamic, wani kamfanin mallakar Maina

Shaidan hukumar yaki da rashawar ta EFCC ya lissafa wadannan kadarorin da matsayin wadanda aka mallaka da kudin sata na al'umma.

Kara karanta wannan

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi

A baya, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari'a a kan zargin ha'inci da ake masa.

Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci jami'an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi. Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.

Kotun ta umarci ya bayyana don ya bayar da hojojin da za su hana a kulle shi ko kuma ya biya naira miliyan 60 na beli ga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel