Daga karshe: WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021 da aka yi

Daga karshe: WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021 da aka yi

  • Hukumar shirya jarabawar WAEC ta sanar da sakin sakamakon daliban da suka rubuta jarabawar a shekarar 2021
  • Kamar yadda shugaban hukumar na Najeriya, Patrick Areghan ya bayyana, ya ce an saki sakamakon jarabawar a yau Litinin
  • Ya sanar da cewa, jimillar dalibai 1,573,849 ne suka yi rijistar jarabawar a Najeriya kuma an samu dalibai 1,560,261 da suka rubuta jarabawar

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma, WAEC, ta saki sakamakon jarabawar da dalibai suka yi ta shekarar 2021.

TheCable ta ruwaito cewa, Patrick Areghan, shugaban hukumar jarabawar ta Najeriya, ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce jimillar dalibai 1,573,849 ne suka yi rijistar jarabawar a fadin Najeriya daga makarantu 19,425 da aka aminta da su. Yayin da dalibai 1,560,261 ne suka rubuta jarabawar.

Daga karshe: WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021 da aka yi
Daga karshe: WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021 da aka yi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda yace, 1,274,784 dalibai sun ci darussa biyar zuwa sama wadanda suka hada da Turanci da kuma lissafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce dalibai 1,560,261 sun ci darussa biyar zuwa sama a wasu darussan da ba Turanci ba da lissafi, TheCable ta ruwaito.

Areghan ya ce hukumar jarabawar ta rike sakamakon dalibai 170,146 da ta ke zargi da magudin jarabawa.

Ya kara da cewa, WAEC a halin yanzu ta gama tantancewa tare da sakin sakamakon dalibai 1,256,990, wanda shi ne kashi 80.56% na daliban da suka zauna jarabawar a Najeriya.

Areghan ya kara da cewa, a halin yanzu hukumar ta na tantance sakamakon dalibai 303,271 wanda ke wakiltar kashi 19.44% na dukkan sakamakon daliban Najeriya.

Hukumar jarabawar ta ce tsaikon da aka samu ya biyo bayan matsalar da wasu dalibai suka samu da darussansu.

Areghan ya kara da cewa, dalibai na bukatar wasu lambobi daga hukumar tare da lambar jarabawarsu domin duba sakamakon ta yanar gizo.

An yi jarabawar wannan shekarar ne tsakanin watan Augusta zuwa na Oktoba, duk da an kammala jarabawar a karshen watan Satumba a Najeriya.

WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa

A wani labari na daban, hukumar shirya jarrabawar ta Yammacin Afirka (WAEC) ta ce ta dage fitar da sakamakon jarrabawar Samun Shaida Kammala Jarrabawa Manyan Makarantun Sakandare (WASSCE) zuwa mako mai zuwa saboda dokar hana fita da aka saka a wasu sassan kasar.

Amma a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis ta ce za ta fitar da sakamakon jarrabawar ne a makon farko na watan Nuwamban shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel