WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa

WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa

- Hukumar Shirya Jarrabawa ta Manyan Makarantun Sakandare na Afirka ta Yamma, WAEC ta dage fitar da sakamakon jarrabawar 2020

- Hukumar ta WAEC ta yi alkawarin fitar da sakamakon jarrabawar na bana cikin kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar

- Amma hukumar ta ce hakan ba zai yi wu ba saboda dokar hana fita da aka saka a wasu jihohin Najeriya makon da ya wuce amma sakamakon zai fito mako mai zuwa

Hukumar shirya jarrabawar ta Yammacin Afirka (WAEC) ta ce ta dage fitar da sakamakon jarrabawar Samun Shaida Kammala Jarrabawa Manyan Makarantun Sakandare (WASSCE) zuwa mako mai zuwa saboda dokar hana fita da aka saka a wasu sassan kasar.

Idan za a iya tunawa hukumar ta ce za ta fitar da sakamakon jarrabawar ne cikin kwanaki 45.

WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa
WASSCE 2020: WAEC ta sanar da sabon ranar da za ta fitar da sakamakon jarrabawa. Hoto daga (pulse.com.gh)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna

Amma a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis ta ce za ta fitar da sakamakon jarrabawar ne a makon farko na watan Nuwamban shekarar 2020.

KU KARANTA: An kama ɗan ƙungiyar asirin da ake nema ruwa a jallo a wurin da akayi fashi da makami a Ogun

Ta rubuta, "Ranar fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE SC 2020: Ya ku dalibai, Hukumar ta yi shirin fitar da sakamakon jarrabawa a yau don cika alkawarin da ta yi na fitar da sakamakon cikin kwanaki 45 amma saboda dokar hana fita da aka saka makon da ta gabata, ta daga zuwa mako mai zuwa, za mu sanar da ainihin ranar nan gaba."

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ƙaryata iƙirarin da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi na cewa ita ce sanadin jinkirin rabon kayan tallafin korona a jihar.

Gwamnan yayin kare gwamnatinsa kan jinkirin rabon kayan tallafin ya ɗora kaifi kan Ministan Jinƙai da Kare Bala'i, Sadiya Umar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164