Bayan wata 4, Boko Haram sun sako jami'in gwamnati da mutum 1 da suka sace

Bayan wata 4, Boko Haram sun sako jami'in gwamnati da mutum 1 da suka sace

  • Boko Haram sun sako jami'in gwamnatin jihar Yobe da abokinsa da suka kwashe watanni hudu a hannunsu bayan sun yi garkuwa da su
  • Miyagun 'yan ta'addan sun sace su a kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu tare da wasu sojoji biyu wadanda suka kashe daga bisani
  • A ranar Alhamis 'yan ta'addan suka sako Mai Lalle da abokinsa duk da babu tabbacin kudi aka biya su ko kuma sako su suka yi kawai

Yobe - 'Yan ta'addan Boko Haram sun sako maza biyu da suka hada da jami'in gwamnatin jihar Yobe, wanda suka sace a watanni hudu da suka gabata.

Ali Shehu wanda aka fi sani da Mai lalle, jami'in gwamnatin jihar ne tare da wani abokinsa mai suna Mustapha wadanda aka sace su tare da wasu sojoji 2 kan abban titin Maiduguri-Damaturu a ranar 24 ga watan Yuli.

Read also

Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe

Daga bisani 'yan ta'addan sun halaka sojoji biyu sannan suka sako magidantan 2 a ranar Alhamis da ta gabata kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Bayan wata 4, Boko Haram sun sako jami'in gwamnati da mutum 1 da suka sace
Bayan wata 4, Boko Haram sun sako jami'in gwamnati da mutum 1 da suka sace. Hoto daga premiumtimesng.com
Source: UGC

Wata majiya daga 'yan uwansu wacce ta bukaci a boye sunanta ta tabbatar wa da Premium Times cewa magidanta biyu har sun hadu da iyalansu a yammacin Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An sako Mai Lalle da Mustapha da yammacin nan kuma yanzu haka sun hadu da iyalansu. An mika su asibiti inda aka duba lafiyarsu," majiyar tace.

A yayin da aka nemi sani ko an biya kudin fansa mai yawa ne ga wadanda suka sace su, majiyar ta waske tare da kin amsawa.

"Abu mafi muhimmacin shi ne yanzu ba su hannun Boko Haram. Dan uwa, mu yi addu'ar kada irin wannan abu ya faru da mu ko wani makusancinmu," yace.

Read also

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Abokai, 'yan uwa da abokan aikin jami'in gwamnatin suna ta murnar sako shi aka yi tun bayan fitar labarin a yammacin Alhamis.

Har a halin yanzu, gwamnatin jihar da 'yan sanda ba su yi tsokaci a kan aukuwar lamarin ba.

'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Islamic State of West Africa Province, ISWAP, sun sace dattijo mai shekaru 50 mai suna Mohammed Askira, tare da 'yan uwansa maza biyu daga gidan sarautar Askira Uba a jihar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, an yi garkuwa da su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan halartar wani taro a garin Askira Uba.

Majiyoyi sun sanar da cewa, dattijon mai shekaru 50 da 'yan uwansa maza biyun da aka sace duk kannai ne ga Mai Martaba Sarkin Askira Uba.

Read also

'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba

Source: Legit.ng

Online view pixel