Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe

Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe

  • Yan ta'addan Boko Haram sun saki wani jami'in gwamnatin jihar Yobe, Ali Shehu Mai Lalle, da abokinsa da suka yi garkuwa da su
  • Mai Lalle da Mustapha sun samu yanci bayan sun shafe kimanin watanni hudu a hannun yan ta'addan
  • Sai dai babu wani jawabi daga mahukunta game da sakin nasu a daidai lokacin kawo wannan rahoton

Jihar Yobe - Kungiyar Boko Haram ta saki ma'aikacin gwamnan jihar Yobe, Ali Shehu Mai Lalle, bayan ya shafe kimanin watanni hudu a hannunsu, jaridar The Nation ta rahoto.

Rahoton ya ce wata majiya ta bayyana cewa Mai Lalle ya samu yanci a yanzu inda ya koma ga iyalansa.

Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, Boko Haram ta saki ma'aikacin gwamnatin Yobe
Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, Boko Haram ta saki ma'aikacin gwamnatin Yobe Hoto: AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Majiyar ta kuma bayyana cewa an saki Mai Lalle ne tare da abokinsa, Mustapha wanda aka sace su tare a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar 24 ga watan Yuli.

Read also

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutuminmu Mai Lalle ya tsira a yanzu yana hannun iyalansa."

Akwai wani rahoto da ba a tabbatar ba cewa an biya makudan kudaden fansa domin sako mutanen biyu amma yan uwa da abokansu sun ki cewa komai a kan haka.

Sai dai babu wani jawabi daga mahukunta game da sakin nasu a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe

A baya mun kawo cewa ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun saki hotunan sojoji biyu da jami’an hulda na Yobe da suka yi garkuwa da su a hanyar babban titin Damaturu/Maiduguri.

Maharan sun kuma saki katin shaidar wadanda suka sace kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A katinan shaidar da suka baje kolinsu, biyu daga ciki mallakar Mai Lalle ne, daya na Mustapha yayin dayan kuma ya kasance na Lpcl Oyediran Adedotun na rundunar Sojojin Najeriya.

Read also

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Source: Legit.ng

Online view pixel