Da dumi-dumi: Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe

Da dumi-dumi: Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe

  • Mayakan Boko Haram da ISWAP sun saki hotunan sojoji biyu da jami’an Yobe da suka yi garkuwa da su
  • A ranar Asabar da yamma ne 'yan ta'addan suka yi ram da mutanen a hanyar babban titin Damaturu/Maiduguri
  • 'Yan ta'addan sun kuma saki katunan shaidan mutanen da abun ya cika da su

Rahotanni sun kawo cewa ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun saki hotunan sojoji biyu da jami’an hulda na Yobe da suka yi garkuwa da su a hanyar babban titin Damaturu/Maiduguri a ranar Asabar.

Maharan sun kuma saki katin shaidar wadanda suka sace kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe
Mayakan sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe Hoto: The Nation
Asali: UGC

A katinan shaidar da suka baje kolinsu, biyu daga ciki mallakar Mai Lalle ne, daya na Mustapha yayin dayan kuma ya kasance na Lpcl Oyediran Adedotun na rundunar Sojojin Najeriya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an sace mutanen hudu a ranar Asabar akan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Yayin da Mai Lalle da Mustapaha suke hanyarsu ta zuwa Maiduguri, su kuma sojojin biyu suna a hanyarsu ta zuwa Kano bayan samun dan gajeren hutu.

An tattaro cewa ba a tuntubi iyalan mutanen da abun ya shafa ba duk da cewar an saki hotunansu.

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

A baya mun kawo cewa jami'an rundunar sojin kasa na Najeriya guda biyu, Bello Abubakar da Oyediran Adedotun sun shiga hannun 'yan bindiga a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a yankin Goni Masari dake Borno.

Sojojin da aka yi garkuwa dasu suna kan hanyarsu ta zuwa Kano ne a wata motar farar hula wurin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, kamar yadda sakon birged ta 29 ya nuna kuma SaharaReporters ta ruwaito.

An gano cewa fasinjojin dake cikin motar sun zargi direban yana da alaka da 'yan bindigan, lamarin da yasa fasinjojin suka sanar da sojojin dake sansanin Mainok.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kanu: An saki Sowore da magoya bayan Nnamdi Kanu bayan sun ci duka

Asali: Legit.ng

Online view pixel