Yunwa: Satar tukunyar abinci a kan murhu ya zama ruwan dare a Enugu, Mutan jihar sun koka

Yunwa: Satar tukunyar abinci a kan murhu ya zama ruwan dare a Enugu, Mutan jihar sun koka

  • Al'ummar wani yanki a jihar Enugu sun bayyana ake satar tukunyar abinci yanzu daga kan murhu
  • Wasu iyaye mata sun bayyanawa manema labarai cewa yanzu zama suke gindin murhu har abinci ya dahu
  • An tattaro cewa bayan satan tukunyar sanwa da ake yi, wasu sun fara fasa shagunan mutane sun kwashe kayan masarufi a jihar

Enugu - Mutan jihar Enugu na kuka kan yadda satar tukunyar abinci; miya, shinka da wake a kan murhu ya zama ruwan dare a unguwanninsu.

Binciken jaridar Leadership ya nuna yadda barayi suke satar tukunyar abinci yayinda ake kan girkawa.

A hirarta da wata mazauniya Obiagu, ya bayyana yadda ya nemi tukunyar abincin da yake girkawa ya rasa daga shiga cikin daki daukan abu.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

A cewarsa:

"Suna na Mrs Ijeomah. Ni mazauniya Ama Awusa ce a Obiagu. Na daura sanwa kan wuta don yarana su ci abinci da yamma. Miyar ta kusa nuna kawai sai nace bari in kara gishiri sai na shiga daki karo gishiri."
"Ina shiga na ji wani kara amma ban taba tunanin wani zai sace tukunyar miya ba. Inda muke zama babu katanga saboda haka kowa na iya shiga. Fitowa na ke da wuya na nemi tukunyar miya na rasa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban ji dadi ba saboda da daren nan yarana kwana sukayi cikin yunwa. Da barawon ya tambayeni da na sammasa."

Yunwa: Satar tukunyar abinci
Yunwa: Satar tukunyar abinci a kan murhu ya zama ruwan dare a Enugu, Mutan jihar sun koka
Asali: Getty Images

Nima haka ya faru da ni?

Wata matar daban kuma wacce ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana yadda akayi awon gaba da miyarta daga kan murhu.

Tace:

Kara karanta wannan

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

"Talauci fa yanzu yayi tsamari. Ta yaya mutum zai shigo gidana na dauke tukunyar miya ddaga kan murhu. Na ji abinda ke faruwa kenan kwanan nan. Yanzu na daina tashi daga bakin murhu idan ina girki."

An tattaro cewa bayan satan tukunyar sanwa da ake yi, wasu sun fara fasa shagunan mutane sun kwashe kayan masarufi a jihar.

Ana kashe mutane, Shugaba Buhari zai yi bayani gaban Allah inji Tsohon Gwamna, Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan matsalar rashin tsaro.

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yace a halin yanzu yankin Arewa maso yamma yana cikin masifa. Bafarawa ya bayyana haka da BBC tayi hira da shi.

Babban ‘dan siyasar ya koka kan halin da mutanen yankin na sa da na shugaban kasa ke ciki. Jaridar Vanguard ta bibiyi hirar da aka yi da Bafarawa jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel