Jarrabawar NECO: Jerin jihohi 4 da aka kwace lasisin wasu makarantu saboda satar amsa

Jarrabawar NECO: Jerin jihohi 4 da aka kwace lasisin wasu makarantu saboda satar amsa

  • Hukumar jarrabawar NECO ta saki sakamakon SSCE na 2021 a ranar Juma'a, 29 ga watan Oktoba
  • Sai dai kuma, hukumar ta kwace lasisin wasu makarantu guda biyar saboda satar amsa
  • Makarantun da abun ya shafa sun kasance a jihohin Bauchi, Kaduna, Katsina da Bayelsa

A ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, hukumar shirya jarabawar fita daga sakandare ta Najeriya (NECO) ta saki sakamakon jarabawar kammala karatun sakandare (SSCE) na shekarar 2021.

Yayin da yake sanar da batun sakin sakamakon, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, shugaban NECO, ya saki wasu kididdiga game da jarrabawar.

Jarrabawar NECO: Jerin jihohi 4 da aka kwace lasisin makarantu saboda yawan satar amsa
Jarrabawar NECO: Jerin jihohi 4 da aka kwace lasisin makarantu saboda yawan satar amsa Hoto: Mohammed Saidu Etsu, Punch Newspapers
Asali: Facebook

Daga cikin bayanan da ya saki, Farfesa Wushishi ya ce an kwace lasisin wasu makarantu na tsawon shekaru biyu a wasu jihohi saboda samunsu da hannu a wajen satar amsa.

Ga jerin jihohin da abun ya shafa a kasa:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

1. Jihar Bauchi (makaranta daya)

2. Jihar Kaduna (makaranta daya)

3. Jihar Bayelsa (makaranta daya)

4. Jihar Katsina (makarantu biyu)

An dakatar da masu sanya ido 20

Shugaban na NECO ya kuma bayyana cewa an dakatar da masu sanya ido su 20 saboda aikata laifuka daban-daban ciki harda "rashin sa ido yadda ya kamata, taimakawa wajen satar jarrabawa, hada kai da wadanda ba dalibai ba wajen rubuta amsa a kan allo, saba ka'idar aiki da kuma karbar cin hanci."

Ya kara da cewar hukumar ta samu rahoto daban-daban na magudin zabe guda 20,003, wanda ke wakiltan 1.63% na wannan shekarar, wanda ya yi kasa da 2.61% da aka samu a 2020.

Farfesa Wushishi ya ce:

"Hukumar na da dadaddiyar al'ada na kin yarda da magudi. Don haka, za a lura cewa lamarin magudi a 2021 ya ragu idan aka kwatanta da na 2020."

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna

Daga yanzu kada a sake bari yan SS1, SS2 su rubuta WAEC, NECO da NABTEB

A gefe guda, mun kawo a baya cewa gwamnatin tarayya ta haramtawa daliban ajin SS1 da SS2 a makarantun Sakandare zama jarabawan waje (external) na WAEC, NECO da NABTEB daga yanzu.

Wannan na kunshe cikin jawabin da ma'aikatar Ilmin tarayya ta saki ga makarantun gwamnatin tarayyar (FGC's).

Jawabin mai lamba: FME/DBSE/US/DOC/III/16 kuma Diraktar ilmin sakandare ta ma'aikatar, Hajiya Binta AbdulKadir, ta rattafa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel