Da duminsa: Daga yanzu kada a sake bari yan SS1, SS2 su rubuta WAEC, NECO da NABTEB

Da duminsa: Daga yanzu kada a sake bari yan SS1, SS2 su rubuta WAEC, NECO da NABTEB

  • Ma'aikatar Ilmi ta saki sabon gargadi kan daliban SS 1 da 2 dake zaman jarabawar karshe
  • Daga yanzu an bada umurnin korar duk dalibin da aka kama ya zana 'External' WAEC, NECO
  • Gwamnati na ganin ire-iren wadannan dalibai ba sa mayar da hankali wajen karatu

Abuja - Gwamnatin tarayya ta haramtawa daliban ajin SS1 da SS2 a makarantun Sakandare zama jarabawan waje (external) na WAEC, NECO da NABTEB daga yanzu.

Wannan na kunshe cikin jawabin da ma'aikatar Ilmin tarayya ta saki ga makarantun gwamnatin tarayyar (FGC's).

Jawabin mai lamba: FME/DBSE/US/DOC/III/16 kuma Diraktar ilmin sakandare ta ma'aikatar, Hajiya Binta AbdulKadir, ta rattafa hannu.

Gwamnatin tarayya tayi barazanar sallamar duk dalibi dan SS1 da SS2 da aka kama ya zauna jarabawa.

Kara karanta wannan

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Wani sashen jawabin yace:

"Ma'aikatar Ilmi ta samu labarin kin bin umurninta na rubuta jarabawan NABTEB (NTC da NBC), WASSCE, NECO (SSCE) da dalibin SS1 da SS2 keyi.
"Daliban da ke irin wannan ba zasu iya natsuwa su yi karatu ba."
"Duk dalibin da aka kama yana rubuta wadannan jarabawa a SS1 da SS2 za'a koreshi daga makaranta."
"Ana bukatar dukkan daliban FGC su bi wannan umurni. Kuma ana baiwa shugabannin makarantu shawaran nuna wa iyaye wannan umurni."

Da duminsa: Daga yanzu kada a sake bari yan SS1, SS2 su rubuta WAEC, NECO da NABTEB
Da duminsa: Daga yanzu kada a sake bari yan SS1, SS2 su rubuta WAEC, NECO da NABTEB
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng