Babu wanda ya cancanci a yi murnar ranar haihuwarsa kamar Mamman Daura, inji Buhari

Babu wanda ya cancanci a yi murnar ranar haihuwarsa kamar Mamman Daura, inji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Mamman Daura murnar maulidin cika shekaru 82 a duniya
  • Ya bayyana Daura a matsayin mutum mai mutunci da basira, kana mai yawan neman ilimi da gaskiya
  • Buhari ya yi addu'o'in alheri da nisan kwana, sannan ya roki Allah ya kara wa Daura karfin yiwa kasa hidima

Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya ya taya Malam Mamman Daura murnar maulidinsa na cika shekaru 82 a duniya.

Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ta shafin Facebook ranar Laraba dauke da sa hannun hadiminsa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi murnar maulidin dan uwa kuma makusancin nasa.

Buhari ya ce babu wanda ya cancanci a taya murnar maulidi kamar Malam Daura.

Babu wanda ya cancanci a yi murnar ranar haihuwarsa kamar Mamman Daura, inji Buhari
Mamman Daura da Buhari | Hoto: thecable.ng
Source: UGC

Ya bayyana Daura a matsayin cikakken mutum mai mutunci, kana mai neman ilimi ga kuma basirar da aiki tukuru.

Read also

Zaben Anambra: Buhari ya taya Soludo murnar lashe zaben gwamnan Anambra

Buhari ya yiwa Daura addu'a cewa:

“Allah ya kara maka lafiya da farin ciki da kuma ci gaba da yi wa kasa hidima. Ina fatan ka kasance lafiya kuma kayi hidimi mafi girma don kasa. Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana."

Buhari ya taya Soludo murnar zama gwamnan Anambra

A wani labarin, Shugaban kasan Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya taya tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo, murnar lashe zaben gwamnan Anambra na 2021.

A ranar Asabar ne aka kada kuri'ar zaben gwamnan jihar Anambra, wanda yayi tsawo sai yau Laraba aka sanar da sakamakon zaben.

Da yake taya Soludo murna, shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

Source: Legit.ng

Online view pixel