Shugaba Buhari ya aikawa takwararsa na Nijar sakon ta'aziyya bisa gobarar da tayi ajalin dalibai 25

Shugaba Buhari ya aikawa takwararsa na Nijar sakon ta'aziyya bisa gobarar da tayi ajalin dalibai 25

  • Daga Faransa, Shugaba Buhari ya aika sakon jaje ga gwamnatin kasar Nijar bisa iftila'in da ya afka musu
  • Mumunar gobara a dakin dalibai tayi sanadiyyar halakar akalla dalibai kananan yara guda 25
  • Shugaban Najeriya ya yi addu'a da jimami ga Gwamnati da Al'umman Ƙasar Jamhuriyar Nijar

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Shugaba Muhammad Bazoum na Nijar sakon ta'aziyya bisa gobarar da tayi sanadin mutuwar daliban makaranta yara 25.

Buhari yayi alhinin mutuwar wannan yara da shekarunsu bai wuce biyar zuwa shida ba.

Wannan Iftila'in Gobaran ya auku ne a ɗakin karatu jihar Maradi dake Kasar.

Garba Shehu ya bayyana sakon ta'aziyyar Buhari a sakon da ya saki ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sarki a Arewa ya tube rawanin sarakuna 4 saboda alaƙa da yan ta'adda

Shugaba Buhari ya aikawa takwararsa na Nijar
Shugaba Buhari ya aikawa takwararsa na Nijar sakon ta'aziyya bisa gobarar da tayi ajalin dalibai 25 Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shugaba Buhari yace,

"Na ƙaɗu matuka da Jin zafi Ƙwarai da wannan Iftila'in wanda ya dauki rayuwar wadan nan yaran Ƴan makaranta.
" Rasuwar wadan-nan Yara Musamman a irin wannan yanayi da suke neman zamo wasu abin bakin ciki ne kwarai, Ina Addu'a da jimami ga Gwamnati da Al'umman Ƙasar Jamhoriyar Niger tare kuma da iyayen yaran dake cikin bakin cikin abinda ya faru."

Asali: Legit.ng

Online view pixel