Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu

Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu

  • Yan ta'addan Boko Haram sun kuma kai wa al'ummar jihar Borno hari da sanyin safiyar yau Laraba
  • Masu idanuwan shaida sun bayyana yadda mutan gari suka gudu daga muhallansu suka shiga cikin dazuka
  • Daga baya abubuwa sun lafa bayan dirar Sojoji wajen kuma mutane sun koma gidajensu

Borno - Mazauna garin Askira a karamar hukumar Askira Uba sun gudu daga muhallansu a jihar Borno sakamakon harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun dira garin ne da safiya kuma suka fara kona gidajen mutane.

Yayinda mazauna suka tsere daga muhallansu zuwa cikin daji da tsaunika, jami'an Sojoji sun isa don ceton rayuwar sarkin garin.

Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu
Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

Daya daga cikin wanda abin ya shafa, Bulama John, ya bayyana cewa ya gudu cikin daji tare da mutane da dama har sai lokacin da abin ya lafa.

A cewarsa:

"Mun gudu cikin daji don ceton rayukanmu; kowa na gudu lokacin da muka samu labarin sun kona Krangila kuma suna hanyar zuwa Askira."
"Daga baya dai mun koma garin, bayan mun ji Sojoji sun shiga bude musu wuta. Sojojin na wajen har yanzu."

Wani direba wanda aka sakaye sunansa yace yana jin harbe-harben bindiga ya gudu da matarsa mai juna biyu.

Har yanzu hukumar Sojoji basu fadi komai kan lamarin ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel