Da duminsa: Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi
- Kotu ta umarci a damko dan Abdulrasheed Maina, Faisal, don a yanke masa hukunci maimakon mahaifinsa
- Hakan ya faru bayan lauyan EFCC, Abubakar Mohammed, ya nemi a kama Faisal a maimakon mahaifinsa
- Ya janyo hankalin alkalin, da cewa Maina da lauyansa sun dade basa bayyana a gaban kotu
A ranar Talata, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari'a a kan zargin ha'inci da ake masa.
Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci jami'an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi. Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.
Kotun ta umarci ya bayyana don ya bayar da hojojin da za su hana a kulle shi ko kuma ya biya naira miliyan 60 na beli ga gwamnatin tarayya.
Hakan ya yi daidai da sashi na 352 (4) na dokar 2015 ta adalci ga masu laifi, Vanguard ta wallafa.
Alkali Abang, ya umarci EFCC da su hukunta dan Maina, a maimakon shi. Umarnin ya biyo bayan lauyan EFCC, Abubakar Mohammed ya nemi hakan.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, bayan Maina da Lauyansa ba su kara bayyana a kotu ba. Sannan Faisal bai kara bayyana a kotu ba tun 24 ga watan Yuni.
KU KARANTA: Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas
KU KARANTA: Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa
A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta bayar da umarnin damkar Sanata Ali Ndume, Sanatan jihar Borno, a kan batan Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa yayin karbar belinsa.
A zaman kotun na ranar Litinin, kotun ta umarci a kamo Ndume saboda rashin bayyana Maina wanda aka yanke wa hukunci a kan damfara.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng