Gyaran hanyoyin wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022

Gyaran hanyoyin wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci amincewar majalisar tarayya akan kashe N5.2b don gyaran wutar fadar sa a 2022
  • An samu wannan makuden ne a cikin kasafin da ya kididdiga ya gabatar wa da majalisar tarayya a watan Oktoba data gabata
  • Wannan kasafi ne da ake yi duk shekara, mutane na ta cece-kuce a kan yawan kudin duk da a shekarar 2021 an ware N3.854b na gyaran

Aso Villa, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na bukatar majalisar tarayya ta amince da kashe N5.2b don gyaran wutar lantarki na fadar shugaban kasa a 2022.

An samu wannan lissafin ne cikin kasafin shekara mai zuwa wacce aka gabatar gaban majalisar tarayya a watan Oktoba, Leadership ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kungiya tana so kotu ta hana Buhari kashe N26bn a kan abinci da zirga-zirga a 2022

Gyaran wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022
Gyaran wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Mutane da dama su na ta surutai a kan yawan kudaden. Duk da dai a shekarar 2021 an ware N3.854b don gyaran wutar lantarkin.

Jaridar Leadership ta ruwaito yadda shugaban kasa zai yi amfani da N21.97b don gina asibiti a cikin fadar ta sa, yanzu haka ana jiran majalisar ta amince.

Baya ga haka, fadar shugaban kasa ta bukaci kashe N104.86m don gyaran ofisoshin da ke fadar.

Wasu kungiyoyi masu zaman kan su sun ce mafi yawan kudaden da ake dankarawa a ayyukan basu dace ba kuma asara ne.

Sun ce a haka ne su ke son ‘yan bindiga su dinga rage kudaden fansar da su ke dankara wa idan su ka yi garkuwa da mutane.

Sannan a wani makamancin labari an samu yadda ma’aikatar noma da bunkasa kauyaku take shirin gina hadaddun ofishin su da N2.5b.

Kara karanta wannan

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A wani labari na daban, Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aike da karin kasafin kudi har N33.8 biliyan gaban majalisar jihar domin ta amince da shi. Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya karanta wannan bukatar a zauren majalisar jihar Kano a ranar Talata.

Kamar yadda bukatar gwamnan ta bayyana, N3.22 biliyan zai biyan ma'aikata yayin da N9.2 za a kashe su kan bukatun yau da kullum, sai kuma N21.5 biliyan ta manyan ayyuka, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da karin kasafin N33 biliyan, jimillar kasafin kudin shekarar 2021 za ta tsaya a N231.7 biliyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel