Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa
- Gwamna Ganduje na jihar Kano ya aike da bukatar karin N33.8 biliyan kan kasafin kudin 2021 gaban majalisar jiha
- Gwamnan ya bayyana cewa N21.5 biliyan daga ciki za a yi amfani da ita wurin karasa manyan ayyuka, sai N3.22 biliyan ta biyan ma'aikata
- Za a samo karin ne ta kudaden shiga na jihar kuma majalisar baki daya ta amince da duba bukatar a zama na gaba
Kano - Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aike da karin kasafin kudi har N33.8 biliyan gaban majalisar jihar domin ta amince da shi. Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya karanta wannan bukatar a zauren majalisar jihar Kano a ranar Talata.
Kamar yadda bukatar gwamnan ta bayyana, N3.22 biliyan zai biyan ma'aikata yayin da N9.2 za a kashe su kan bukatun yau da kullum, sai kuma N21.5 biliyan ta manyan ayyuka, Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da karin kasafin N33 biliyan, jimillar kasafin kudin shekarar 2021 za ta tsaya a N231.7 biliyan.
Ganduje ya yi bayanin cewa, an miko wannan bukatar ne saboda bukatar da ta taso tabbatar da an cimma manufofi da kuma kammala ayyuka masu matukar amfani.
Kamar yadda takardar ta bayyana, za a yi amfani da kudaden shiga da aka samu tare da sauran hanyoyin da gwamnati ke bi wurin tabbatar da an samu karin kasafin kudin.
Majalisar baki daya ta amince da duba karin kasafin kuma za ta dauka mataki a zama na gaba da za ta yi.
Majalisar ta kafa kwamitin bincike kan KSSHT
A wani bangare na daban, majalisar ta kafa kwamiti domin ya duba zargin da ake wa makarantar fasahar jinya ta jihar Kano da tatsar dalibai tare da kuma karbar kudaden makaranta ba tare da bayar da rasit ba.
Wannan ya biyo bayan bukata mai amfani da Alhaji Salisu Ibrahim ya mika gaban majalisar kuma Alhaji Nuhu Achika ya goyi bayan ta.
Ganduje ya sake korar tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji, daga mukaminsa
A wani labari na daban, A karo na biyu a cikin shekara daya, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya, daga mukamin da ya nada shi.
Da farko, gwamnan ya sallami Magaji yayin da ya ke kwamishina bayan ya yi wata wallafar jin dadi kan mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu sakamakon cutar korona da yayi fama da ita.
Amma kuma, bayan watanni kadan, Ganduje ya sake bai wa Magaji wani mukami, Daily Trust ta ruwaito. An nada shi a matsayin shugaban aikin bututun iskar gas da kuma kwamitin masana'atun na jihar Kano.
Asali: Legit.ng