Ku biya mu kudinmu, Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya domin karbar cin hanci

Ku biya mu kudinmu, Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya domin karbar cin hanci

  • An samu masu kada kuri'a da suka siyar da kuri'unsu a wasu rumfunan zabe a wannan zaben gwamnan da ake yi a jihar Anambra
  • Kamar yadda majiyoyi masu yawa da suka zanta da Legit.ng suka sanar, da yawa daga cikin manyan jam'iyyun sun siya kuri'u
  • A takaice dai, an samu wasu masu kada kuri'a da suka bi wakilan jam'iyya suna bukatar kudinsu bayan kada kuri'a da suka yi

Anambra - Daya daga cikin babbar matsalar da ke cigaba da haifar da matsala a Najeriya shi ne siyan kuri'a, wanda kuma ya cika a zaben gwamnan jihar Anambra.

Wakilan jam'iyyun siyasa da ke kare ra'ayoyin jam'iyuunsu an zargesu da bai wa masu kada kuri'a kudi daga dari biyar har zuwa dubu goma.

Ku biya mu kudinmu, Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya domin karbar cin hanci
Ku biya mu kudinmu, Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya domin karbar cin hanci
Source: UGC

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, an ga wani wakilin jam'iyya na ganawa da masu kada kuri'a bayan saka kuri'unsu tare da rubuta sunayensu a wata takarda, alamu da ke nuna za a biya su daga baya.

Read also

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

Amma kuma, masu kada kuri'a da ke biye da shi sun ta ihun a biya su hakkinsu a take.

Wannan al'amarin ne ya faru a kusan dukkan rumfunan zabe kamar yadda majiyoyi da ke lura da zaben suka tabbatar.

Jaridar Sahara Reporters ta yi ikirarin cewa, wasu daga cikin wakilan jam'iyyu sun biya dubu goma inda wasu suka biya har dubu shida kan kuri'a daya.

Duk da babu takamaiman jam'iyyar da suka siya kuri'a, an gano cewa kusan dukkan jam'iyyun siyasan ne suka dinga siyen kuri'un.

Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki

A wani labari na daban, Charles Soludo, dan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), har yanzu bai kada kuri'a ba.

Read also

'Yan sanda sun ceto malaman UNIAbuja da aka sace, an kama 'yan bindiga

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya isa rumfar zabensa da wuri amma ya kasa saka kuri'arsa saboda rashin aikin na'urar BVAS a wurin.

Dan takarar APGA din ya ce zai zanta da manema labarai bayan ya kada kuri'arsa cike da nasarar. Kamar yadda rahoto ya bayyana, a lokacin, mutum tara kacal ne daga cikin sama da dari bakwai suka saka kuri'arsu a rumfar zaben.

Source: Legit.ng

Online view pixel