Matawalle: Masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa da ke daukan nauyinsu

Matawalle: Masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa da ke daukan nauyinsu

  • Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce masu kaiwa yan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa
  • Gwamnan ya ce wasu daga cikin masu kwarmatawa yan bindigan bayanai sun ce yan siyasa ne ke ɗaukan nauyin su
  • Matawalle ya ce ƴan siyasan tunda farko ba su son shirin sulhu da afkuwar da gwamnati ta yi a jihar ya yi nasara

Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce wasu mutane da ke aiki da ƴan bindiga sun amsa cewa yan siyasa ne ke ɗaukan nauyin su, rahoton Daily Trust.

Gwamnan, wanda ya furta hakan yayin hira da wata gidan rediyon Legas, RadioNow ta yi da shi bai bayyana sunayen ƴan siyasan da ƴan bindigan suka tona wa asiri ba.

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Kan Hanya: Barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai

Matawalle: Masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa da ke daukan nauyinsu
Masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai sun tona asirin wasu ƴan siyasa da ke daukan nauyinsu, Matawalle. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ita ma ta ruwaito cewa ya kuma yi magana kan yadda wasu manyan yan siyasa suka riƙa yi wa shirin yi wa ƴan bindiga afuwa zagon ƙasa.

Ya ce:

"Bayan mun fara tattaunawar, ka san ya kamata a samu hadin kai tsakanin gwamnati, mutanen jihar da sauran manyan yan siyasa.
"Abin takaici, a yayin da gwamnati ke ƙoƙarin samar da zaman lafiya, wasu manyan ƴan siyasa suna tunanin ba su son mu yi nasara."
"Sun rika yin maganganu marasa amfani kan sulhun da tattaunawar. Wasu daga cikinsu na da alaƙa da ƴan bindigan kuma sun rika hure musu kunne cewa kada su yarda da afuwan na gwamnati."

Ya cigaba da cewa:

"Muna da bayanai. An kama wasu masu kai wa ƴan bindiga bayanai, muna da fiye da 2000 a hannun jami'an tsaro, kuma wasun su sunyi magana sun tona asirin wasu.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja

"Sun ce wasu ƴan siyasan ne ke ɗaukan nauyin su, suna ce musu gwamnatin jiha da tarayya ba za su cika alƙawarin da suka yi musu ba."

An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa

A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel