Sojoji za su fara tura mutum-mutumin ‘Robots’ domin su yaki ‘Yan ta’adda a Najeriya

Sojoji za su fara tura mutum-mutumin ‘Robots’ domin su yaki ‘Yan ta’adda a Najeriya

  • Sojojin Najeriya suna shirin kirkiro na’urorin da za su taimaka wajen yakar matsalar rashin tsaro.
  • Hukumomin NITDA da NCAIR ne za su taimakawa jami’an tsaron wajen cin ma wannan burin na su.
  • Shugaban NACEST, Janar Yahaya H Abdulhamid ya kai wa shugaban NCAIR ziyara a kan batun

Benue - Sojojin Najeriya na kokarin komawa amfani da mutum-mutumi watau Robots da sauran na’urorin kimiyya da fasaha wajen magance rashin tsaro.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar NITDA da NCAIR za su hada-kai domin kirkiro sababbin hanyoyin da za a shawo kan matsalar tsaro a kasa.

Wadannan hukumomi da ke kawo cigaba ta fuskar fasahar IT da kuma kirkire-kirkiren mutum-mutumi za su bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya.

Rahoton ya ce wannan yunkuri da za a yi zai taimaka sosai wajen samar da bayanan da suka danganci sha’anin tsaro ta hanyar cin moriyar fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Shugaban hukumar NCAIR na kasa, Injiniya Ya’u Garba Isa ya bayyana wannan a lokacin da ya gana da shugaban makarantar sojoji ta NACEST a Benuwai.

Shugaban NACEST, Birgediya Janar Yahaya H Abdulhamid ya kai wa Injiniya Ya’u Isa ziyara a ofishinsa da ke birnin Makurdi, Benuwai a ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojoji
Mutum-mutumi watau Robots a fim Hoto: www.express.co.uk
Asali: UGC

NITDA, NCAIR za su taimakawa sojoji

A jawabin da Isa ya fitar, yace za su hada-kai da sojoji domin kirkiro na’urorin da za su yaki miyagu.

Shugaban hukumar yace an kafa NCAIR ne domin bincike da kirkiren zamani, tana yin aiki ne fasahar AI, mutum-mutumi da IOT, da sauran cigaba na Duniya.

Sahara Reporters tace za a tura wadannan robots masu kama da mutane zuwa filin yaki domin su kawo karshen ‘yan ta’adda, da duk wasu miyagun ‘yan bindiga.

“NCAIR na kokarin samar da kirkire-kirkire, salon kasuwancin zamani, samar da aikin yi, da kawo cigaban kasa.”

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Najeriya 5 da ke jan ragamar shugabancin wasu manyan hukumomin duniya

Cibiyar za ta duba yiwuwar samar da bam na komguta da zai yi aiki da fasahar WLAN a fagen fama.” - Ya’u Isa

Kasafin 2022: N570bn ba za su ba - COAS

A makon nan ne shugaban hafsun Sojoji, Janar Farouk Yahaya ya sanar da Sanatoci cewa kudin da aka warewa Rundunar Najeriya a kasafin 2022 sun yi kadan.

Abin da sojoji za s kashe a shekara mai zuwa ba zai zarce N570bn ba. A halin yanzu Najeriya tana fama da ‘Yan ta’adda, ‘Yan bindiga da kuma masu tada kayar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel