N570bn da za a bamu, ba za su isa a yaki ‘Yan ta’adda ba – Hafsun Soja ya fadawa Majalisa

N570bn da za a bamu, ba za su isa a yaki ‘Yan ta’adda ba – Hafsun Soja ya fadawa Majalisa

  • Hafsun Sojojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Farouk Yahaya, ya bayyana gaban ‘yan majalisar dattawa
  • Janar Farouk Yahaya ya kai kuka gaban Sanatoci yayin da yake kare kasafin kudin gidan soja na 2022
  • Shugaban sojojin yace an zaftare N140bn daga cikin kudin da suke bukata domin yakar ‘yan ta’adda

FCT, Abuja - Sojojin kasan Najeriya sun koka game da kasafin kudin kasa, inda suka bukaci a cire su daga tsarin kason kudin da ma’aikatar kasafin kudi take yi.

Jaridar Punch ta rahoto shugaban hafsun sojojin kasa, Laftanan Janar Farouk Yahaya ya na wannan kira a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dattawa.

Janar Farouk Yahaya ya shaidawa ‘yan majalisa cewa Naira biliyan 579 da aka warewa sojojin kasa ba zai isa su yaki matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata

“A lokacin da ake tsara kasafin kudin 2022, sojojin kasa sun bukaci Naira biliyan 710.” - Janar Farouk Yahaya
Sai a karshe ma’aikatar kudi, kasafi, da tsare-tsaren tattalin arziki ta rage abin da muka gabatar zuwa N579bn.”
Hafsun Sojoji
Lokacin da Farouk Yahaya ya zama Laftanan Janar Hoto: Bashir Ahmaad / Facebook
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kudin ba za su isa ba - Janar Farouk Yahaya

A rahoton da Tribune ta fitar a ranar Laraba, an ji hafsun sojin yana kukan cewa wannan mataki da aka dauka yana da tasiri a wajen yakin da ake yi.

“Majalisar tarayya ta lallabi ma’aikatar kudi, ta cire sojoji daga tsarin kasafin da ta ke kai, wanda ake bada kason kudi sannu-sannu.” – Yahaya.

Yahaya yace fitar da kudi da wuri a kasafin shekarar 2022 zai taimaka masu wajen sauke nauyin da ke kansu na samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Najeriya 5 da ke jan ragamar shugabancin wasu manyan hukumomin duniya

Janar Farouk Yahaya yana so a daina kacancana kasonsu a 2022, a ba sojoji kudinsu tun farkon shekara.

A cewarsa, wannan zai taimaka wajen gyara gidajen sojoji da suke cikin barikoki 138, sannan a horas da jami’an tsaro, a kuma iya sayen isassun kayan aiki.

An kashe 'yan bindiga a Kaduna

A ranar Laraba aka ji cewa Dakarun Sojojin sama sun hallaka ‘Yan bindiga yayin suka yi ruwan wuta a wasu kauyukan jihar Kaduna a tsakiyar makon nan.

Gwamnatin Kaduna ta bada sanarwa inda kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a yammacin jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel