Kaduna: Rayuka 8 sun salwanta, 46 sun jigata sakamakon gobara

Kaduna: Rayuka 8 sun salwanta, 46 sun jigata sakamakon gobara

  • Mutane takwas ne suka sheka lahira yayin da wasu arba'in da shida suka jigata sakamakon gobara a jihar Kaduna
  • Daraktan hukumar kashe gobara ta Kaduna, Paul Aboi, ya ce an ceci mutum 17 a cikin gobarar da aka yi daga Yuni zuwa Oktoba
  • A cewarsa, an tseratar da kayan N1.1 biliyan yayin da kadarori masu darajar N2.4 biliyan suka salwanta

Kaduna - Rayuka takwas ne suka salwanta yayin da wasu 46 suka samu miyagun raunika a gobara 140 da aka yi a jihar Kaduna tsakanin watan Yuni da Oktoba, kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta sanar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Paul Aboi, wanda ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Alhamis, ya ce an ceci rayuka 17 a yayin gobarar.

Read also

Karin bayani: Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas

Kaduna: Rayuka 8 sun salwanta, 46 sun jigata sakamakon gobara
Kaduna: Rayuka 8 sun salwanta, 46 sun jigata sakamakon gobara. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Kamar yadda yace, shida daga cikin mace-macen sun auku ne a gobara 57 da aka yi a jihar tsakanin watan Yuli da Augusta, Daily Trust ta wallafa.

"Kadarori da suka kai darajar N1.1 biliyan aka tseratar da gobarar a cikin wannan lokacin yayin da kadarorin N2.4 biliyan gobarar ta lamushe," yace.

Aboi ya kara da cewa, an samu jimillar gobara dari da arba'in a Kaduna, Zaria da Kafanchan, inda yace hukumar ta yi bakin kokarin ta wurin ganin hakan ya ragu ta hanyar wayar da kan mutane wurin kiyaye gobarar.

Ya dora laifin gobarar a kan nuna halin ko in kula tare da amfani da kayayyakin lantarki ba yadda ya dace ba. Ya jaddada cewa mazauna yankin su kiyaye wurin amfani da kayayyakin wutar lantarki.

Read also

Rahoto: Yadda gobara ta kone mutane 10 tare da lalata miliyoyi a Kano

Gwamnatin Kaduna ta fallasa hanyoyi 6 da 'yan bindiga ke samun kudin shiga

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta fallasa inda miyagun 'yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.

Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar tace, shi ne wurin karbar kudin fansa daga 'yan uwan wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar kuma Daily Trust ta samu kwafi.

Source: Legit.ng

Online view pixel