Da duminsa: Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra

Da duminsa: Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra

  • Hukumar INEC a yau, 4 ga Nuwamba, ya fara rabon kayan zabe zuwa kananan hukumomin jihar Anambra
  • Ana fitar da kayan zaben daga hedkwatar bankin Najeriya CBN dake Awka, babbar birnin jihar Anambra
  • Masu lura na gida da na waje na wajen rabon kayayyakin domin ganewa idanuwansu abubuwan dake gudana

Akwa, Anambra - Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta fara rabon kayayyakin zaben gwamnan jihar Anambra da aka shirya yi ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, 2021.

An fara rabon kayayyakin zuwa kananan hukumomin jihar 21, Legit ta ruwaito.

Jami'an hukumar INEC yanzu haka suna harabar hedkwatar bankin Najeriya CBN dake Anambra inda akayi ajiyan kayayyakin.

Wadanda ke hallare a wajen sun hada da wakilan jam'iyyun siyasa da kuma shugaban kwamitin yada labarai na INEC, Festus Okoye.

Read also

Zaben Anambra: Yan takarar gwamna 9 sun yi kira ga sakin Nnamdi Kanu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra
Da duminsa: Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra
Source: UGC

KAI TSAYE: Saura kwana 2 zaben Anambra, yan takara sun taru a daki daya don tabbatar da babu rikici

Dukkan yan takara a zaben Gwamnan jihar Anambra, sun rattafa hannu kan takardar tabbatar da an yi zaben ranar 6 ga Nuwamba cikin zaman lafiya.

Wannan taro ya gudana ne a Cibiyar tunawa da Dora Akunyili dake Awka, jihar Anambra.

Kwamitin zaman lafiya ta Najeriya NOC karkashin jagorancin Janar Abdusalami Abubakar (Rtd)

Wakilin Legit.ng na taron kuma mun kawo muku bayanai kai tsaye.

Jerin manyan yan takara kujeran gwamnan jihar guda 9

1. Ben Etiaba, dan takarar AA

2. Farfesa Charles Soludo, APGA

3. Obinna Uzoh, SDP

4. Akachukwu Nwankpo, ADC.

5. Onyejegbu Okwudili, APM

6. Sanata Ifeanyi Uba, YPP

7. Sanata Andy Uba, APC

Read also

A dage zaben gwamnan Anambra domin kare rayuka – Babban fasto ga FG

8. Nnamdi Nnawuo, PRP

9. Obiora Okonkwo of the ZLP.

Source: Legit.ng

Online view pixel