Matsolo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta

Matsolo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta

  • Yan sandan Ogun sun kama wata matar aure Memunat Salaudeen ta da dauki hayar wasu maza uku don su taya ta yin garkuwa da mijinta.
  • Asirinsu ya tonu ne a yayin da yan sanda suka kama matasan uku dauke da adda da kuma igiya sannan suka musu tambayoyi
  • Memunat ta ce ta yanke shawarar yin garkuwa da mijinta ne domin shi matsolo ne, kuma tana son ta karbi kudi a hannunsa ko ta wane hali

Ogun - Yan sanda a jihar Ogun sun kama wata matar aure Memunat Salaudeen kan zarginta da hada baki da wasu mutane uku don yin garkuwa da mijinta, rahoton Daily Trust.

Yan sanda masu sintiri a manyan hanyoyi ne suka kama wadanda ake zargin yayin da suke bincika motocci a kan hanyar Papa/Itori.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin jami’ar Abuja

Matsalo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta
An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa yan sandan sun kama maza uku - Olayinka Lawal, Asungba Nura da Usman Oluwatoyin kan babur kuma suka tsayar da su.

A cewarsa, yayin bincikarsu an gano adda da sabuwar igiya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Oyeyemi ya ce yan sandan sun raba su sannan suka musu tambayoyi kan abinda suke niyyar yi da addan da igiyan.

Mazan uku duk sun bada amsoshi daban-daban a cewar Oyeyemi hakan yasa aka zurfafa bincike.

Ya cigaba da cewa:

"Bayan tsananta tambayoyi, mazan uku sun amsa cewa wata mata mai suna Memunat Salaudeen ne ta basu N8000 su siyo adda da igiyar da za a iya daure dan adam da shi.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

"Sun kara da cewa matar, wacce ma'aikaciyar jinya ce a unguwar Balogun tuntun Gas line Ifo, ta umurci su boye a wani hanya, za ta biyo da mijinta ta wurin sai su kama shi su daure sannan su bukaci kudin fansa."

Miji na matsalo ne, baya bani kudi, Memunat

Kakakin yan sandan ya ce matar auren wacce kuma ma'aikaciyar jinya ne ta amsa cewa ita ce ta kitsa yadda za a yi garkuwar.

Oyeyemi ya ce:

"Ta shaidawa yan sanda cewa mijinta baya bata kudi hakan yasa ta kitsa wannan garkuwar domin ta banbari kudi a hannunsa ko ta wane hali ne."

Kwamishinan yan sandan jihar CP Lanre Bankole ya bada umurnin a mayar da wadanda ake zargin sashin binciken masu garkuwa don zurfafa bincike.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

Kara karanta wannan

Da Dumi: An tsinci gawar ƴan bindiga 3 da suka kashe kansu wurin faɗan rabon kuɗin fansa a wata jihar Arewa

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel