Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi

Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi

  • Gwamna Zulum na jihar Borno ya sake bude titin Bama zuwa Banki mai nisan kilomita 76 wanda aka rufe saboda 'yan Boko Haram
  • Zulum ya bayyana cewa, ya yi hakan ne domin farfado da lamurran kasuwanci tsakanin yankin da kasashe masu makwabtaka
  • Zulum ya sanar da cewa noma ya dawo da kashi 600 a wannan shekarar, wanda ake sa ran shekara mai zuwa za a samu fiye da hakan

Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake bude titin Bama zuwa Banki mai nisan kilomita 76 domin farfado da lamurran kasuwanci tsakanin Najeriya da kasashe masu makwabtaka irinsu Kamaru da Chadi.

An rufe titin a shekarar 2012 sakamakon hauhawar al'amuran 'yan ta'addan Boko Haram.

Daily Nigerian ta wallafa cewa, a yayin jawabin bikin budewar a ranar Laraba a Bama, Zulum ya ce babu wani cigaba da za a samu wurin farfado da yankin ba tare da an dawo da lamurran kasuwanci ba.

Read also

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi
Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

Ya jinjina wa mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya mayar da hankali wurin farfado da zaman lafiya a jihar Borno, Daily Nigerian ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya bayyana cewa kokarin da sojojin Najeriya ke yi a jihar ne ya kawo karuwar fadadar ayyukan gona a wannan shekarar wanda a baya ba a iyawa.

"A wannan shekarar, yankunan da aka noma a Borno sun karu da kashi 600. Nan da shekara mai zuwa, za mu iya samun fiye da abinda muka samu a wannan shekarar," Zulum yace.

A yayin jawabin marabansa, shugaban karamar hukumar Bama, Aji-Koli Kachalla, ya jinjina wa cigaban da aka samu inda ya kwatanta cewa wannan babban abun jin dadi ne ganin al'amuran kasuwanci sun dawo.

A yayin jawabinsa, shugaban rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Christopher Musa, ya ce wannan cigaban wata nasara ce ta rundunar sojin wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar da sauran sassan arewa maso gabas.

Read also

Karin bayani: Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas

Musa ya jinjina wa gwamnati da jama'ar Borno kan hadin kai da goyon bayan da suke bai wa rundunar soji da sauran cibiyoyin tsaro.

Ya tabbatar da cewa, rundunar sojin za ta cigaba da sauke nauyin da ke kanta.

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Islamic State of the West African Province, ISWAP, sun sace fasinjoji biyar a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Talata da ta gabata.

PRNigeria ta tattaro cewa, lamarin ya auku wurin karfe 3 na yammaci a Tamsukau da ke karamar hukumar Kaga, wacce ke da nisan kilomita 7 daga Ngamdu, babban sansanin sojin Najeriya.

'Yan ta'addan da ke sanye da kayan sojojin Najeriya sun kafa wurin bincike a kan titi wanda hakan yasa masu kaiwa da kawowa suka yi zaton sojoji ne.

Source: Legit.ng

Online view pixel