Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

  • 'Yan ta'addan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri
  • Mummunan al'amarin ya auku ne wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata da ta gabata a Tamsukau da ke Kaga
  • Ana zargin Abou Aseiya ne ya kaddamar da farmakin, sabon Ameerul Fiya da aka nada domin kula da Sambisa

Maiduguri, Borno - 'Yan ta'addan Islamic State of the West African Province, ISWAP, sun sace fasinjoji biyar a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Talata da ta gabata.

PRNigeria ta tattaro cewa, lamarin ya auku wurin karfe 3 na yammaci a Tamsukau da ke karamar hukumar Kaga, wacce ke da nisan kilomita 7 daga Ngamdu, babban sansanin sojin Najeriya.

'Yan ta'addan da ke sanye da kayan sojojin Najeriya sun kafa wurin bincike a kan titi wanda hakan yasa masu kaiwa da kawowa suka yi zaton sojoji ne.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi masu karfi sun sanar da PRNigeria cewa 'yan ta'addan sun yi awon gaba da ababen hawa uku da fasinjoji amma daga bisani sai suka sako ababen hawan da wasu fasinjoji kuma suka rike biyar daga ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce: "Ana zargin Abou Aseyia da kai wannan farmakin, wanda a cikin kwanakin nan aka nada shi a matsayin Ameerul Fiya wanda ke kula da dajin Sambisa."

Kwamandan 'yan ta'dddan ya bayyana tafe da motocin yaki 13, MRAP biyu da motar da harsashi ba ta bulawa.

Sun kai farmakin da basu samu nasara ba a Ngamdu, Katarko a jihar Yobe da karamar hukumar Damboa inda aka halaka 'yan ta'addan masu tarin yawa.

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

A wani labari na daban, Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da rundunar Operation HADIN KAI sun halaka wasu 'yan ta'adda tare da samo a kalla motocin yaki biyu tare da buhunan taki 622 da suke amfani da shi wurin hada bama-bamai.

Kara karanta wannan

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

An halaka 'yan ta'addan a sassa daban-daban na jihar Borno da suka hada da kauyukan: Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da Kijmatari duk a jihar Borno da kuma titunan Ngala zuwa Wulgo da Nguru zuwa Kano.

Mukaddashin yada labaran tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel