Yanzu-Yanzu: An bindige jami'an tsaro uku yayin da mayakan ISWAP suka kai sabon hari Borno

Yanzu-Yanzu: An bindige jami'an tsaro uku yayin da mayakan ISWAP suka kai sabon hari Borno

  • Wasu yan ta'adda da ake zargin mayaƙan kungiyar ISWAP ne sun hallaka jami'an yan sanda biyu da soja guda ɗaya a jihar Borno
  • Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da yan ta'addan suka yi kokarin kutsa wa garin Malamfatori, jami'an tsaron suka tarbe su
  • Garin dai na ɗaya daga cikin yankunan jihar Borno da yan Boko Haram suka maida hedkwatar su a baya

Borno - Premium Times tace akalla jami'an yan sanda biyu da soja ɗaya aka kashe yayin wata gwabzawa da mayakan ISWAP a Malamfatori, jihar Borno.

Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa jami'an da suka rasu, suna cikin haɗakar jami'an tsaro dake aikin kakkaɓe ragowar yan ta'adda a yankin, a wani shiri na dawo da yan gudun hijira gidajensu.

A ranar Laraba da muke cike da yamma, yan ta'adda da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka yi kokarin kutsa kai don tilas su shiga garin.

Kara karanta wannan

Aƙalla mutum 7 suka mutu yayin da miyagun yan bindiga suka kai harin farko yankin wannan jihar

Wata majiya daga cikin jami'an tsaron, yace:

"Yayin wata musayar wuta da muka yi yau a garin Malamfatori, mun rasa jami'an tsaro uku, yan sanda biyu da kuma soja ɗaya."
Sojoji
Da Zafinsa: Aƙalla Dakarun yan sanda 2 da soja ne suka mutu yayin musayar wuta da mayaƙam ISWAP a Borno Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wane irin makamai yan ta'addan suka zo da shi?

Jami'in tsaron ya kuma ƙara da cewa sojoji da sauran jami'an tsrao da aka tura yankin, sun gamu da cikas na hari, kuma sun maida martani.

"Mayakan ISWAP sun zo da muggan makamai kamar motocin yaƙi masu ɗauke da bindigun kakkaɓo jirgi."
"Jami'an tsaron dake cikin tawagar sun haɗa da sojoji, yan sanda, yan sa'kai, kuma sun samu nasarar daƙile harin.

Ina ne garin Malamfatori?

Malamfatori, na ɗaya daga cikin yankunan jihar Borno da mutanen ciki suka watse saboda yawan hare-haren yan ta'adda, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Shugaban hukumar leken asiri

Ba da jimawa ba Gwamna Babagana Umaru Zulum ya ziyarci garin, domin karban yan gudun hijira tare da maida su gidajensu a hukumance.

Mutane na kallon garin Malamfatori a matsayin hedkwatar majalisar Shura na yan ta'addan Boko Haram, saboda haka ake ganin nan ne sansanin mayaƙan Boko Haram.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa yankin Malamfatori baki ɗayansa yana ƙarƙashin ikon kungiyar ISWAP ne a yanzu.

A wani labarin kuma yayin da labarin mutuwar kasurgumin ɗan bindiga Dogo Gide ta karaɗe kafafen watsa labarai, mun gudanar da bincike kan sahihancin labarin.

A cewar labaran da ake yaɗawa mataimakinsa ne ya bindige shi har Lahira, to amma shin dagaske haka ta faru?

Bincike daga masana da kuma masu rubutu a kan al'amuran yan bindiga a Arewa ta yamma ya tabbatar da abinda ke faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel