Za'a naɗa shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, wata babbar Sarauta a Arewa

Za'a naɗa shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, wata babbar Sarauta a Arewa

  • Mai martaba sarkin Argungu, Alhaji Sama'ila Mera, zai naɗa shugaban majalisar dattijai sarautar 'Ganuwan Kabi' ranar Jumu'a
  • Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa, Sanata Yahaya, tare da wasu wakilan masarauta ne suka jagoranci sanar da Lawan
  • Za'a gudanar da wannan naɗin sarauta ne a wani ɓangare na bikin cikar Sarkin Argungu shekara 25 a kan karagar mulki

Kebbi - Sarkin Argungu, HRH Alhaji Samaila Muhammadu Mera da yan majalisun masarautar Argungu, zasu naɗa shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, sarautar gargajiya.

Leadership ta ruwaito cewa masarautar zata naɗa shi 'Ganuwan Kabi' wato mai kare martabar masarauta.

A wata sanar wa da mai taimaka masa ta bangaren watsa labarai, Ola Awoniyi, ya fitar ranar Laraba, yace za'ayi naɗin sarautar ne a wani ɓangare na bikin cikar sarki shekara 25 da hawa karagar mulki.

Read also

Da Duminsa: Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokoki, sun hana yan majalisu shiga

Sanata Ahmad Lawan
Sarkin Argungun Zai naɗa shugaban majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, Saurautar 'Ganuwan Kabi' Hoto: thewhistler.ng
Source: UGC

Ɗaya daga cikin jagororin majalisar dattijai, sanata Yahaya Abubakar Abdullahi, tare da wakilan sarki ne suka kaiwa Lawan katin gayyata zuwa taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin Lawan zai yi wani abu ne bayan naɗin?

Ana tsammanin shugaban majalisar zai dira garin Argungu tun ranar Alhamis domin kaddamar da wasu muhimman ayyukan sanata Yahaya Abdullahi.

Sanata Yahaya, yana wakiltar mazaɓar Kebbi ta Arewa a majalisar dattijan tarayyan Najeriya a halin yanzu.

Hakanan kuma Sanata Ahmad Lawan zai halarci ɗaura auren ɗaya daga cikin ɗiyar mai martaba sarkin Argungu, mai suna Habiba.

Za'a gudanar da ɗaura auren ne a babban masallacin Jumu'a na Muhammad Mera dake cikin garin Argungu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga

Read also

Cika shekaru 15 kan mulki: Takaitaccen tarihin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar

Rikici dai yaƙi ci yaƙi cinyewa a majalisar tun bayan tsige kakakin majalisar, Ayuba Abok, tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda.

A halin yanzun babu ɗan majalisar da zai shiga zauren har sai mambobin sun warware matsalolin dake tsakanin su.

Source: Legit.ng

Online view pixel