Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota

Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota

  • Rayuka 5 sun sheka lahira sakamakon mummunan hatsarin mota da aka gwabza a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano
  • Mota kirar Volkswagen ta ci karo da adaidaita sahu a kan titin Kwanar Dumawa zuwa Kunya da ke Minjibir inda mutum 2 suka jigata
  • Kwamandan FRSC na yankin ya tabbatar da cewa tsabar gudun ababen hawan ce ta sanya mummunan hatsarin na ranar Talata

Minjibir, Kano - Rayuka biyar sun salwanta, wasu biyu sun samu miyagun raunika a mummunan hatsarin da aka yi wanda ya hada da wata mota kirar Volkswagen da adaidaita sahu kan titin Kwanar Dumawa zuwa Kunya a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano.

Mummunan hatsarin da ya auku a ranar Talata, ya ritsa da fasinjojin da ke kan hanyarsu ta zuwa kauyukan da ke kusa da wurin, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota
Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kwamandan hukumar kula da hadurra na yankin, Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsabar gudun ababen hawan.

Ya ce rayuka biyar da suka hada da maza hudu da mace daya sun rasa rayukansu yayin da wasu maza biyu suka samu miyagun raunika, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace, bayan samun rahoton hatsarin, tawagarsa da ke ofishin Minjibir sun isa wurin kuma sun kwashe mutanen zuwa manyan asibitocin Minjibir da Danbatta inda likitoci suka tabbatar da mutuwar biyar daga ciki.

Biyun da a halin yanzu suka jigata sakamakon raunikan da suka samu, suna asibiti inda suke samun kulawar masana lafiya, ya kara da cewa.

"Mun samu kira wurin karfe 1 da minti 5 na ranar Talata. Muna samun labarin muka hanzarta tura jami'ai da ababen hawa wurin hatsari domin ceto jama'ar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

"Sun isa wurin karfe 1 da minti goma na rana kuma sun kawar da duk wani cunkoso.
“Bayan sun isa asibitin, likitan da ke aiki a lokacin ya tabatar da mutuwar mutum biyar daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su," Mato yace.

Ya kara da cewa, ababen hawan biyu da hatsarin ya ritsa da su suna da lambar rijista kamar haka: DUT449 CZ da GWL 51 WG.

A makon da ya gabata, wani makamancin hatsarin ya faru a arewacin Kano. Dalibai biyar daga kwalejin horar da malamai ta Sa'adatu Rimi da ke Kano sun rasa rayukansu yayin da wasu suka jigata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel