Kotu ta yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos

Kotu ta yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos

  • Wata kotu da ke zamanta a Kasuwan Nama, Jos, jihar Plateau ta yanke wa wani matashi daurin watanni shida saboda satar akuya
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun yadda matashin mai shekaru 25, Abbas Isaiah ya kutsa gidan mai akuyan ya sace ta
  • Bayan amsa laifinsa, kotu ta yanke wa Abbas Isaiah hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ko tarar N15,000

Jos - Wata babban kotun yanki da ke zamanta a Kasuwan Nama, Jos, a ranar Litinin ta yanke wa wani mutum mai shekaru 25, Abbas Isaiah daurin wata shida a gidan yari saboda satar akuya.

Alkalin kotun, Mista Lawan Suleiman ya yanke wa Isaiah hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa bisa ruwayar NewsWireNGR.

Kotu ta yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos
An yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos. Hoto: NewsWireNGR
Source: Facebook

Alkalin ya bawa Isaiah zabin biyan tarar N15,000.

Read also

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar NewsWireNGR ta rahoto cewa Alkalin ya ce hukuncin zai zama darasi ga wasu da ke niyyar aikata irin wannan laifin.

Har gida Isaiah ya tafi ya sace akuyar

Tunda farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Monday Dabit, ya shaidawa kotun cewa wani Nwosoghunnaya Uchechi ne ya kai korafi caji ofis na Anglo-Jos a ranar 15 ga watan Oktoba.

Dabit ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya sace akuyar ne a gidan mai akuyan a inda ta ke kiwo.

Mai gabatar da karar ya ce an kwato akuyar wadda darajar ta ya kai N16,000 daga hannun Isaiah a yayin bincike.

Monday Dabita ya ce laifin da aka aikata ya saba da tanadin sashi na 277 na dokar Penal Code na jihar Plateau bisa ruwayar NAN.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Read also

Matashin da ya yi wuf da wayoyin karuwai 2 bayan ya kai su otal yin lalata, an damkeshi

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Source: Legit.ng

Online view pixel