Kaduna: Kotu ta umurci gidan jarida ta biya El-Rufai N10m saboda wallafa labaran ƙarya a kansa

Kaduna: Kotu ta umurci gidan jarida ta biya El-Rufai N10m saboda wallafa labaran ƙarya a kansa

  • Wata babbar kotu da ke zama a Kaduna ta yanke wa wani gidan jarida hukuncin biyan gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna N10,000,000
  • Hakan ya biyo bayan yadda jaridar ta wallafa labarin kanzon kurege akan kadarorin El-Rufai a shekarar 2015, inda ta ce yana da kudi N90bn da gidaje 40
  • Bayan kammala hukuncin ne El-Rufai ya ce ya yi hakan ne don ya bayyana wa marubuta cewa damar rubutu ba damar bata wa mutane suna da yi musu sharri ba ce

Kaduna - Wata babbar kotu da ke zama a Kaduna ta yanke wa kamfanin buga labarai na Today da ke da gidan jaridar The Union, hukuncin biyan Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna N10m kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Read also

Kotu ta yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos

Kaduna: Kotu ta umurci gidan jarida ta biya El-Rufai N10m saboda wallafa labaran ƙarya a kansa
Kotu ta umurci gidan jarida ta biya El-Rufai N10m saboda wallafa labaran ƙarya a kansa. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Hakan ya biyo bayan yada labaran kanzon kurege akan sa da gidan jaridar ya yi, har ila yau The Cable ta bayyana yadda kotu ta umarci gidan jaridar da ta ba shi hakuri a bayyane.

Dama El-Rufai ya maka gidan jaridar a kotu ne bayan sun wallafa wani labarin kage akan dukiyoyin da ya mallaka.

A ranar 2 ga watan Yulin 2015, gidan jaridar The Union su ka wallafa wani labari a bangon jaridar su inda su ka ce gwamnan ya bayyana cewa ya mallaki N90bn da manyan gidaje 40.

A hukuncin da Alkalin Kotun, Mairo Muhammed ta yanke, ta ce wadanda ake zargin sun bata sunan gwamnan.

Gidan jaridar ya yi ta yada labarin ga jama’a

Kotun ta sanar da cewa El-Rufai ya nuna yadda kamfanin jaridar ya dinga yada wa mutane labarin a gari.

Read also

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

Kamar yadda Alkalin ta ce:

“El-Rufai ya nuna cewa be bayyana kadarorin sa masu kimar N90bn da hamshakan gidaje 40 ba, wanda hakan ya nuna zancen kanzon kurege ne kuma an yi ne don bata ma sa suna.”

Lauyan El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha ya kwatanta hukuncin a matsayin hukunci mafi adalci.

Bayan kammala shari’ar gwamnan ya ce damar rubutu ba damar yi wa mutane kage bane ko kuma ‘yan jarida su dinga zubar wa jama’a mutunci.

El-Rufai da kan sa ya je kotun don tabbatar da karar sakamakon yadda ya yarda da adalcin shari’a, wanda yin hakan ya tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro.

Ya ce hakan zai zama izina ga sauran gidajen jaridu don su san yadda kotu ta ke yanke hukunci akan bata sunan jama’a.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

Read also

Gwamnan Gombe ya bukaci a kwashe tubabbun 'yan Boko Haram a kaisu jami'ar soji

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Source: Legit.ng

Online view pixel