ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

  • Hukumar yaki da rashawa mai zaman kan ta, ICPC ta ce ta kwato gidaje 301 daga hannun wasu jami'an gwamnati 2 a Abuja
  • Shugaban ICPC, Bolaji Owasanoye ya bayyana hakan a gaban kwamitin majalisar wakilai na kula da dillalai a FCT
  • Ya ce mahandama na amfani da harkar wurin wawurar kudade tare da narka su wurin siyan gidaje da filaye

Abuja - Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC ta ce ta samo gidaje 301 da aka wawuri kudi aka siya daga jami'an gwamnati a babban birnin tarayya na Abuja, TheCable ta wallafa.

Bolaji Owasanoye, shugaban hukumar ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da kwamitin majalisar wakilai na wucin-gadi suka shirya kan ayyukan masu siyar da filaye da gidaje a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja
ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A yayin jawabi a taron, Owasanoye ya ce hukumar ta samu korafi daban-daban kan ayyukan handama.

Ya ce rashin rijistar gidaje da filaye a babban birnin tarayya yadda ya dace ne ya janyo rashawa a bangaren, TheCable ta wallafa.

"Duk da ba mu da jimillar yawan matsalolin da suka shafi filaye, mun samu korafi daga masu ruwa da tsaki a harkar gidajen, masu siya da kuma jama'ar gari kan yadda dillalan ke cuta a ciki da wajen Abuja," yace.
“Wadannan korafe-korafen suna da yawa. Sun hada da sa hannun bogi, siyar da fili ga mutane da yawa, bada fili ba tare da amincewar minista ba, kwace filaye ba tare da bin hanyar da ya dace ba da sauran kalubale makamantan hakan.
“Sai kuwa jami'an gwamnati masu handamar kudaden su na amfani da harkar wurin boye dukiyar sata da boye kudade. Su kan yi amfani da harkar wurin siyan filayen suna adanawa da kudin sata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

"Hukumar ta kwato gidaje 241 daga jami'in gwamnati inda ta sake kwato wasu gidaje 60 daga wani jami'in," yace.

Hakazalika, Daniel Esei, mataimakin daraktan EFCC ya ce ya dace a karfafa hukumar ta dinga daukan mataki kan wadanda ta kama da boye kudaden haram.

EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, bayan an titsiye shi na kwanaki biyu kan zargin rashawa.

Lauyansa, Mike Ozekhome ne ya sanar da Premium Times hakan a ranar Laraba.

Hukumar ta tsare Anyim tun daga ranar Lahadi kuma aka sako shi kan belinsa da hukumar ta bayar a ranar Talata, kamar yadda Ozekhome, SAN, ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel