An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma na kudi N21.9bn mai gado 14 a Aso Rock

An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma na kudi N21.9bn mai gado 14 a Aso Rock

  • Bayan gabatar da bukatar gina asibitin alfarma a majalisa, an kaddamar da ginin asibitin ba tare da bata lokaci ba
  • An fara ginin ranar 1 ga Nuwamba, 2021 kuma za'a kammala ranar 1 ga Nuwamba, 2022.
  • Shugaban ma'aikatan Buhari yace Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da iyalansu da kuma wasu jami'an gwamnati zasu yi amfani da shi.

Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Litinin ya jagoranci bikin kaddamar da ginin asibitin alfarma mai gao 14 kacal a fadar Aso Villa.

Wannan asibiti da za'a gina zai ci akalla bilyan 21.

A jawabin da ya gabatar a bikin fara ginin, Gambari ya bayyana cewa idan aka kammala ginin wasu zababbun mutane zasu amfana da katafaren asibitin, rahoton Thisday.

A cewarsa, Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da iyalansu da kuma wasu jami'an gwamnati zasu yi amfani da shi.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Najeriya 5 da ke jan ragamar shugabancin wasu manyan hukumomin duniya

A kalamansa:

"Muna farin cikin yin abinda na gobe har wadanda ba' haifa ba yanzu zasu amfana da shi."
"Mun san muhimmancin kiwon lafiya ga rayuwar dan Adam kuma gwamnati za ta cigaba da samarwa yan Najeriya ingantaccen kiwon lafiya."

Gambari ya yi kira ga wadanda aka baiwa kwangilan su hanzarta saboda a kammala aikin cikin lokacin da aka kayyade.

An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma a Aso Rock
An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma na kudi N21.9bn mai gado 14 a Aso Rock Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya amince a gina asibiti mai gado 14 a kudi N21.9billion a Aso Villa

Mun kawo muku cewa, shugaba Buhari ya amince da a gina sabon asibiti mai gado 14 kacal a fadar shugaban kasa Aso Villa a kudi N21 billion.

Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Umar Tijjani, ya bayyana hakan ga mambobin kwamitin daidaito na majalisar dattawa yayin bayani kan kasafin kudin N40 billion na fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

Wani kamfani aka baiwa kwangilan kuma yaushe za'a kammala?

Umar Tijjani ya bayyana cewa kamfanin Julius Berger Nigeria, JBN, aka baiwa kwangilan ginin asibitin kuma za'a fara ginin ranar 1 ga Nuwamba, 2021, riwayar DailyNigerian.

Ya bayyanawa kwamitin cewa an zabi baiwa JBN kwangilan ne saboda su suka gina fadar shugaban kasan kuma suke kula da ita tun shekarar 1990.

Ya kara da cewa za'a kammala ginin cikin shekara guda kuma a bude asibitin ranar 31 ga Disamba, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng