An kwato bama-bamai daga hannun mayakan Nnamdi Kanu na ESN a jihar Anambra

An kwato bama-bamai daga hannun mayakan Nnamdi Kanu na ESN a jihar Anambra

  • Rundunar 'yan sanda ta gano wasu kayan fashewa da ake zargin na mayagan ESN ne
  • An gano muggan makamai da sauran kayayyakin aikata laifi a cikin wata jaka a wani wurin da aka kai hari
  • A halin yanzu, rundunar na ci gaba da bincike don gano asalin masu wadannan kaya domin a kamo su

Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce an gano wasu bama-bamai da aka kera a cikin gida daga hannun 'yan ta'adda masu goyon bayan Nnamdi Kanu, ESN, The Cable ta ruwaito.

A cewar NAN, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, Aderemi Adeoye, ya ce an gano bama-baman da suka hada da “Bom na RPG da kuma gurneti” a wurin da aka kai hari a Afor Nnobi a karamar hukumar Idemili ta kudu ta jihar Anambra.

Read also

'Yan sanda sun yi ram da masu samar da kayan shaye-shaye da barasar bogi mai cutarwa

Da yake magana a ranar Litinin din da ta gabata, Adeoye ya ce an yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga, inda ya kara da cewa an gano kayayyakin ne a cikin wata jaka da aka gudu aka bari a wurin da aka kai harin.

An kwato bama-bamai daga hannun mayakan Nnamdi Kanu na ESN a jihar Anambra
'Yan sandan Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Ya kuma ce an tura jami’an wata runduna da ke kwance bama-bamai zuwa wurin.

A cewar Adeoye:

“Rundunar ta gano wani bam kiran gida na RPG da kuma gurneti a wurin da aka yi artabu tsakanin ‘yan bindiga da ake zargin mayakan ESN ne da kuma ayarin jami’an tsaro na hadin gwiwa da kwamishina ya jagoranta da kansa."
“An tura jami’an tsaro domin gudanar da bincike a wurin da aka yi harbe-harben don gano alamun da za su taimaka wajen binciken da nufin gano sunayen ‘yan bindigar da kuma manufar ‘yan bindigar.

Read also

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

“An gano wadannan abubuwa ne a cikin wata jaka wadda kuma tana dauke da wata wayar hannu da gurneti guda daya da aka kera a gida da kuma Bam din Roka."

Da yake bayyana kudirin rundunar na tabbatar da tsaro a jihar, ya ce babban sufeton ‘yan sandan ya umarci jami’ansa da su tabbatar da kare lafiyar ‘yan kasa a lokacin zaben gwamna da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa, Echeng Echeng, kwamishinan ‘yan sanda na Anambra, ya yaba da hadin kai tsakanin sojoji, ‘yan sanda, DSS da sauran jami’an tsaro kan inganta tsaro a jihar.

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

A wani labarin, Rundunar yan sandan Benue ta ja hankalin mazauna jihar kan wani sabon salon ta’addanci da wasu da ba’a san ko su wanene ba ke amfani da shi wajen kashe mutanen da suka shiga hannunsu.

Read also

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan jan hankali da ‘yan sandan suka yi baya rasa nasaba da kisan wata matashiya.

An dai tsinci gawar matashiyar ne a ranar Lahadi a kusa da tsohuwar gadar da ke sada mutum da yankin 'North Bank' na Makurdi, babbar birnin jihar.

Source: Legit.ng

Online view pixel