Bidiyon biloniyan duniya Jeff Bezos ya na jinjina wa shugaba Buhari

Bidiyon biloniyan duniya Jeff Bezos ya na jinjina wa shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu ya samu jinjina kan tsarin shugabancinsa tare da yadda ya mayar da hankali kan sauyin yanayi
  • Babban biloniyan duniya dan asalin kasar Amurka kuma shugaban Amazon, Jeff Bezos a ranar Litinin ya jinjina wa Buhari a Glasgow, Scotland
  • 'Yan Najeriya masu yawa sun dinga martani kan wannan cigaban inda wasu ke ta jinjina wa shugaban kasan kan kokarinsa

Glasgow, Scotland - Biloniyan Amurka kuma mamallakin Amazon, Jeff Bezos, a ranar Litinin 1 ga watan Nuwamba a Glasgow da ke Scotland ya jinjina wa shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya kwarzanta shi kan yadda ya ke habaka lalatattun filaye a kasar Najeriya inda ya kwatanta kokarinsa na farfado da fili mai girman kadada miliyan hudu da babban lamari.

Read also

Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Bezos ya bi ayarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasan Faransa Emmanuel Macron, Yarima Charles da shugaban kasan Maritania Mohammed Ould Ghazouani a taron COP 26.

Bidiyon biloniyan duniya Jeff Bezos ya na jinjina wa shugaba Buhari
Bidiyon biloniyan duniya Jeff Bezos ya na jinjina wa shugaba Buhari. Hoto daga Femi Adesina
Source: Facebook

A yayin yabo tare da jinjina ga shugaban kasan Najeriya a taron da shugaban kasan Faransa, takwaransa na kasar Maritania da Yarima Charles suka dauka nauyi, mamallakin Amazon ya ce:

"Mun yi matukar sa'ar samun shugaban kasa Buhari na Najeriya a tare da mu a yau. Najeriya ta taka babbar rawa wurin dawo da tsarin kuma ta dauka alkawarin gyaran kadada miliyan hudu ta filayen da suka lalace
‘‘Wannan burin da kasar da ta fi kowacce tattalin arziki a Afrika ta bayyana ya nuna yadda lamarin ke da muhimmanci."

'

Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

Read also

Thebo Mbeki: Yadda na yi kutun-kutun na hana Obasanjo zarcewa karo na 3

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Glasgow, Scotland don halartan taron COP26 na taron gangamin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi.

Hadimin Shugaban kasan na kafafen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan ne a bidiyon da ya saki ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021.

Buhari zai gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.

Source: Legit.ng

Online view pixel