Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Glasgow, Scotland don halartan taron COP26 na taron gangamin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi.

Hadimin Shugaban kasan na kafafen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan ne a bidiyon da ya saki ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021.

Buhari zai gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.

Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin
Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin Hoto: Presidency
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon:

Source: Legit.ng

Online view pixel