Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya yau Lahadi, daga nan kuma ya tafi Faransa

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya yau Lahadi, daga nan kuma ya tafi Faransa

  • Daga dawowarsa daga kasar Saudiyya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake shillawa kasar waje
  • Buhari zai kai ziyara kasashe biyu; Birtaniya da Faransa inda zai kwashe kwanaki kafin ya dawo
  • Fadar Shugaban kasa bata bayyana ranar da Shugaban kasan zai dawo daga wannan tafiya ba

Abuja - Kwana biyu bayan dawowa daga Saudiyya, Shugaba Muhammadu Buhari zai garzaya birnin Glasgow, Scotland don halartan taron COP26 na taron gangamin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi.

Mai magana da yawun shugaban kasan ya bayyana cewa Buhari zai gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Lahadi, 31 ga Oktoba, 2021.

A cewarsa:

"Shugaba Muhammadu Buhari ranar Lahadi, 31 ga Oktoba zai tashi daga Abuja zuwa Glasgow, Scotland don halartan taron gangamin masu ruwa da tsaki na shirin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi."

Kara karanta wannan

Labari Cikin Hotuna: Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu ya dira Fadar Shugaba Buhari Aso Villa

"Buhari ya shirya gabatar jawabi ga shugabannin kasashe ranar Talata."

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya yau Lahadi
Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya yau Lahadi Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Wa ya shirya taron?

Garba Shehu ya ce Gwamantin kasar Birtaniya tare da hadin kan gwamnatin kasar Italiya ne suka shiyrya taron domin tattaunawa wajen cimma yarjejeniyar Paris.

Hakazalika yace, Shugaba Buhari zai halarci wasu taruka tare da Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, da Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.

Buhari ya samu rakiyar Ministan wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanayi, Sharon Ikeazor; NSA Babagano Munguno; DG NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

Daga nan kuma zai garzaya Faransa

Garba Shehu ya bayyana cewa bayan taron sauyin yanayi a Birtaniya, Shugaba Buhari ya tafi kasar Faransa domin halartan taron zaman lafiya a Paris.

Yace:

"Shugaba Buhari daga baya zai tafi Paris, Faransa domin ziyara ga Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, domin nuna godiya bisa ziyarar da Shugaban kasan Faransan ya kawo Najeriya a baya."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

"Kuma zai halarci taron zaman lafiya Paris 2021, karo na hudu da Shugaban kasar Faransa ke shiryawa."

Yaushe zai dawo?

Mai magana da yawun Buhari bai bayyana lokacin da Shugaban kasan zai dawo ba idan ya tafi yau.

Legit Hausa ta yi yunkurin tuntubar fadar shugaban kasa domin sanin yaushe zai dawo amma abin ya ci tura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel