Karuwai sun lakadawa matar aure dukan tsiya a kan kwastomansu mijin matar

Karuwai sun lakadawa matar aure dukan tsiya a kan kwastomansu mijin matar

  • Wata matar aure ta kwashi kashinta a hannu, yayin da karuwai suƙa taru suka mata dukan kawo wuka a Otal
  • Rahoto ya bayyana cewa matar ta je Otal ɗin ne domin tabbatar da abinda take zargi a kan mijinta na zuwa wurin karuwa
  • Magidancin ne dai ya kasance yana zuwa wurin wata karuwarsa yayin da yake wa matarsa ƙaryan cewa harkokin kasuwanci ne suka yi masa yawa

Oyo - Wasu mata masu zaman kansu sun haɗu sun lakaɗawa matar aure dukan tsiya saboda ta zo neman mijinta, wanda kwastoma ne.

Aminiya ta rahoto cewa matar taje neman maigidan nata ne a wani Otal dake tasar mota a Birnin Badun Jihar Oyo, bayan samun labarin yana zuwa.

Wata majiya a tashar motar, wadda aka ɓoye bayananta saboda wasu dalilai, tace matar Bahaushiya ce kuma mijin nata ma Bahaushe ne.

Read also

Kishi Kumallon Mata: Wata Budurwa ta daba wa Saurayinta wuka daga duba WhatsApp dinsa

Matsalolin Aure
Karuwai sun lakadawa matar aure dukan tsiya a kan kwastomansu mijin matar Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Meya kawo faɗa har da duka?

Majiyar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Magidancin yana zuwa wurin wata karuwarsa ya kwana, yayin da yake wa matarsa ta sunnah ƙaryar cewa harkokin kasuwanci ne suke hana shi dawowa gida."
"Da matar taga abin ya yi yawa shine taje har Otal ɗin ta gane wa idonta, domin tana zargin can yake zuwa, kuma daga zuwa ta gan shi ya na kwance a gadon karuwa."
"Zuwan matarsa yasa karuwar ta faɗa wa kwastoman ya daina zuwa wurinta domin ba ta son wani abu ya haɗa ta da matarshi."

Shin ya daina zuwa?

Majiyar ta ƙara da cewa magidanci bai daina zuwa kwana wurin wannan mata mai zaman kanta ba, hakan ya sa matar ta dawo a karo na biyu.

"Da matar da sake dawowa ta yi kokarin cewa wajibi mijinta ya zo su tafi gida kafarta kafar shi amma yace sam ba zai tafi ba."

Read also

Mijina ya mun barazanar kashe ni da 'ya'yana kuma ba abinda za'a yi, Mata ta nemi Kotu ta datse igiyoyin aurenta a Abuja

"Hakan ya harzuƙa matar, ta fara bugun ɗaya daga cikin karuwan, nan take suƙa taru suka mata dukan tsiya, har sai da aka kaita asibiti."

A wani labarin kuma Wata Budurwa ta daba wa Saurayinta wuka daga duba WhatsApp dinsa

Wata dalibar kwalejin fasaha ta caka wa saurayinta wuka bayan duba irin firar da yake da wasu mata a WhatsApp.

Dalibar dake karatun aikin jarida a kwalejin jihar Delta, ta aikata wannan aika-aika ne a ranar Laraba da ta gabata.

Source: Legit.ng

Online view pixel