Abuja: Jami'an tsaro sun cafke 'yan mata 27 yayin samame da suka kai gidan magajiya

Abuja: Jami'an tsaro sun cafke 'yan mata 27 yayin samame da suka kai gidan magajiya

  • Ma’aikatan ofishin samar da walwalar FCT Abuja, tare da jami’an tsaro sun kai samame wani fitaccen gidan karuwai da ke Abuja, inda su ka kama a kalla karuwai 27
  • Amar, wanda ya jagoranci samamen ya ce ministan Abuja, Dr Ramatu Aliyu ta yanke shawarar yaki akan duk wasu masu harkoki a gidajen karuwai da masu karuwanci a fadin birnin tarayya
  • Ya ce ministan Abuja ce ta bayar da umarnin kawo karshen duk wani aiki na rashin da’a a cikin birnin kamar karuwanci, kuma gidajen karuwai ne sanadin yaduwar cutar COVID-19

Abuja - Ma’aikatan ofishin samar da walwalan babban birnin tarayya, Abuja, tare da taimakon jami’an tsaro sun kai samame wani fitaccen gidan karuwai a Abuja, SaharaReporters ta ruwaito.

Sun kama a kalla karuwai 27, a cewar mukaddashin darektan samar da walwalar na FCT Abuja, Sani Amar wanda ya jagoranci samamen a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

Abuja: Jami'an tsaro sun cafke 'yan mata 27 yayin samame da suka kai gidan magajiya
Jami'an tsaro sun cafke 'yan mata 27 yayin samame da suka kai gidan magajiya a Abuja. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Bisa ruwayar SaharaReporters, Amar ya ce ministan Abuja, Dr Ramatu Aliyu ta yi kira akan yaki da duk wasu masu harkoki a gidan karuwai da karuwan a cikin babban birnin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa, ministan ce ta umarci darektan ofishin samar da walwalar akan kawo karshen duk wasu abubuwa na hayaniya kamar masu saide-saiden kan hanya da gidajen karuwai.

Amar ya kara da bayyana yadda za a mika duk karuwan da aka kama zuwa ga ‘yan sanda don a yanke mu su hukunci.

Ya ce ministan FCT Abuja a shirye ta ke da ta tabbatar an bi doka a cikin birnin domin hakan na cikin dokar Penal Code din arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa dokar hukumar kula da shige da fice da dokar NAPTIP ta nuna harkokin gidajen karuwai, saide-saiden bakin hanya, karuwan kan titi, cutar da yara, azabtar da yara da satar yara a matsayin ta’addanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Kamar yadda Amar ya ce:

“Ministan Abuja, Dr Ramatu Aliyu da sakataren FCT, Mr Olusade Adesola da mukaddashin sakataren SDS, Dr Kelvin Ike duk sun hada kai wurin kulawa da lafiya da rayukan mazauna Abuja.
“Ministan ta yanke hukuncin yaki da ma’aikatan gidan karuwai a Abuja, kuma ta bayar da umarnin kawo karshen ayyukan su a garin.
“A bayyane yake, yadda ministan ta jajirce akan yin ayyuka tukuru don tabbatar da dokokin FCT.”

Ya ce duk karuwai su canja sana’a

Bisa wannan da ne darektan ya kara da rokon jama’a musamman masu harka da gidajen karuwai da su kan su karuwan a kan canja ra’ayin su da kuma sana’ar su.

Kamar yadda ya ce:

“Annobar COVID-19 gaskiya ce kuma ya kamata duk masu harka da karuwai da karuwan su samu lokaci don su duba lafiyar su.
“Ta wannan hanyar ne a ke yada cutar COVID-19 kuma aikin shugabannin FCT ne su kula da lafiya da rayukan mazauna yankin.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Bidiyon yadda wata jarumar Kannywood ta yi wa Daso ta-tas akan rawar TikTok

A jiya, kun ji cewa wata jarumar Kannywood ta fito fili ta fadi abinda ya ke damun ta dangane da Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso a wani bidiyo da NaijaFamily su ka wallafa a shafin su na Facebook.

Jarumar wacce ba ta shahara kwarai ba ta bayyana takaicin ta da alhini akan yadda Daso ta ke kwasar rawa a shafin ta na TikTok inda ta ce ya kamata manyan Kannywood su fada ma ta gaskiya.

A cewar ta, Daso ta na zubar da mutuncin yaran ta, jikokin ta, zuri’ar ta da kuma su ‘yan Kannywood don haka ya kamata ta gyara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel