Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye sabbin mahaddatan Al-Qur'ani kimanin 2,500 a Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye sabbin mahaddatan Al-Qur'ani kimanin 2,500 a Bauchi

  • Kamar yadda aka saba lokaci bayan lokaci, babban Malamin addini kuma jagoran Tijjaniya Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye dalibai
  • Sheikh Dahiru Bauchi na da dalibai da manyan makarantu a jihohin Najeriya daban-daban inda ake haddar Al-Qur'ani
  • Malamin ya ja hankalin daliban kan muhimmancin bibiyar abinda suka haddace akai-akai

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sake yaye dalibai 2,438 da suka kammala haddar Al-Qur'ani mai girma da kuma dalibai 226 suka sauke karatun amma basu haddace ba.

Aminiya ta ruwaito cewa wadannan dalibai sun yi karatu ne a makarantun babban Malamin dake ciki da wajen Najeriya.

Daliban jihohin Najeriya daban-daban ne aka yaye a wannan bukin Walima.

Jihohi da adadin dalibansu

Jihar Bauchi: Mahaddata 534, masu sauka 226

Jihar Katsina: Mahaddata 499

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana

Jihar Kano: Mahaddata 385

Jihar Kaduna: Mahaddata 257

Jihar Jigawa: Mahaddata 186

Jihar Sakkwato: Mahaddata 168

Jihar Zamfara: Mahaddata 152

Babban Malamin ya samu wakilcin babban dansa, Ibrahim Sheikh Dahiru, a taron.

Ya ja hankalin daliban su kara zage damtse domin inganta tilawarsu, inda ya ce Alkur’ani abu ne da in mutum ya sauke ko ya haddace ana so kullum ya rika bibiyarsa yana yawan karantawa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye sabbin mahaddata
Sheikh Dahiru Bauchi ya yaye sabbin mahaddatan Al-Qur'ani kimanin 2,500 a Bauchi Hoto: Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel